Yanda Kasuwar Saye Da Sayarwa a Harakar Kwallo Ke Gudana.

Da Farko Zakuji Cewa Real Madrid, Barcelona Harda Ma Bayern Munich Duk Suna Rababin Daukar Matashin Dan Wasan Borussia Dortmund Mai Suna Jadon Sancho.

Kungiyar Kwallon Kafa Ta Liverpool Na Zawarcin Dan Wasa Timo Werner Dan Asalin Kasar Germany, Werner Wanda Qungiyoyi Da Dama Irinsu Liverpool, Bayern Munich Da Manchester United, Ke Sa Ido Wurin Son Daukar Matashin Dan Wasan.

Jaridar (Sky Italy) Ta Bayyana Cewa Chelsea Kan Iya Mika Dan Wasanta Alvaro Morata Domin Daukar Dan Wasan Kasar Argentina Gonzalo Higuan a Watan January.

Juventus Tasa Ido Akan Matashin Dan Wasan Ajax Matthijis Delight Dan Kasar Netherland.

Paris Saint Germany Ta Fara Duba Yiyuwar Dauko Dan Wasan Tsakiyar Everton Mai Suna Idrissa Gueye, Anasa Ran Idrissa Gueye Shine Wanda Zai Maye Gurbin Dan Wasa Adrien Rabiot Wanda Ke Yunkurin Canza Sheka Daga Paris Saint Germany Zuwa Qungiyar Kwallon Kafa Ta Barcelona a Watan January Ko a Karshen Season Dinnan.

Real Madrid Na Shirye Shiryen Ta Mikawa Chelsea Tayin Yasan Ta Guda Isco Alcaron Da Matteo Kovatic, Duk Dan Qungiyar Ta Sallamar Musu Da Eden Hazard Dinda Suka Juma Suna Nema, Kovatic Wanda Yake a Matsayin Aro Wato Loan a Qungiyar Kwallon Kafa Ta Chelsea, Real Madrid Na Son Yin Amfani Dashi Wurin Cinma Burinta Na Son Daukar Dan Wasa Eden Hazard a Watan January Ko a Karshen Season Dinnan.

Qungiyar Kwallon Kafa Ta Chelsea Karkashin Jagorancin Maurici Sarri Ta Shirya Kawo Yan Wasa Guda Hudu a Wannan Watan Na January, Cikin Yan Wasan Sun Hada Da Nabil Fekir Na Lyon, Sai Jamie Vardy, Gonzalo Higuan Da Isco Alcaron, Amman Ana Tunanin Higuan a Matsayin Aro Zasu Dauke Shi.

Daga Jaridar #Marca

Labarinda Muke Samu a Safiyar Yau Zakuji Cewa Qungiyar Kwallon Kafa Ta Barcelona Ta Baiwa Coach Din Ta Dama Daganan Zuwa Watan #February Yayi Gaggawa Ya Yanke Shawara a Kan Zai Tsaya a Qungiyar Yaci Gaba Da Aiki, Ko Kuma Zai Tafi Ne Karshen Wannan Kakar Da Muke Ciki 2018/2019 Season.

To Fans Ya Kamata Musan Cewa Nemanda Barcelona Takewa Coach Din Sassaulo #De Zerbi, Bawai Yana Nufin Basuson #Valverde Da Yaci Baba Da Kasancewa a Qungiyar Ba, Shi #Valverde Din Shine Yake Fargaba Akan Zaman Sa Qungiyar Ne Saboda Baaga Wata Alama Wajen Valverde Din Ba Tason Cigaba Da Aiki a Qungiyar Bane.

Ina Addua Allah Ya Dawo Mana Dashi a Barcelona Inji #ARTHUR MELO.

Dan Wasan Tsakiya Na Barcelona Dan Wasa Mai Shekaru 22 Yana Tunanin Dawowar Neymar Jr Qungiyar Zaifi Qarko Daci Gaba Kamar Yadda Ya Bayannawa Manema Labarai Wato #MUNDO-DEPORTIVO.

Kalaman Arthur Melo Zuwa Ga Neymar Jr, Ina Addua Gareshi Akan Yadawo Barcelona Domin Dan Wasane Mai Daraja Zai Taimakawa Qungiyar Ta Kowane Hali, Bansaniba Ko Akwai Wani Dalili Da Zai Sashi  Kin Dawowa Qungiyar Ta Barcelona, Neymar Jr Ya Kasance Babban Abokine Ga Dan Wasa Na Barcelona Domin Kuwa Yana Matukar Son  Arthur Melo Din Ta Hakane, Ta Hakane Yake Shirin Jawo Hankalin Neymar Da Yadawo Tsohuwar Qungiyar Shi.

Messi Da Barcelona a Shekarar 2018

Qungiyar Barcelona Ta Samu Nasarori Da Dama a Shekarar 2018, Qwamushe Kofin Laliga Da Sambade Kofin Copa Del Rey,  Dadin Dadawa Gashi Kuma Haryanzu Sune Akan Table Din Laliga, Haka Kuwa Ta Samu Galaba Akan Abokiyar Hamayya Wato Real Madrid, Shine Ya Bata Dama Ta Iya Zuwa Qwallaye 147 a Wannan Shekara Ta 2018.

Messi Ya Kammala Shekarar 2018 Da Kwallaye 47 Da Bada Gudummuw Wato Assist 23, Wannan Ya Nuna Cewa Yanada Hannu a Cikin Rabin Kwallayen Da Barcelona Taci Guda 147 a Wannan Shekarar

Messi Din Shine Kan Gaba a Shekarar 2018 Wajen Zura Kwallaye a Gasar Laliga Ta Wannan Season, Ya Antaya 15 goals Dukda Cewa Ya Rasa Wasu Wasanni Sakamakon Injury Dinda Yaje a Wasansu Da Sevilla.

Labari Daga Wata Jarida Ta Kasar France Wato TeleFoot, Ta Rawaito Cewa Dan Wasan PSG Adrien Rabiot Yaki Karbar Tayi Daga Wasu Qungiyoyi Na Kasar Turai, Kamar Chelsea Tottenham Da Kuma Juventus, Domin Nuna Damuwa Akan Ganin Yazo Barcelona a Watan January Mai Kamawa, Dan Wasan Ya Kulla Yarjejeniya Pre Contract Da Qungiyar Ta Barcelona To Amma Dole Qungiyar Sai Ta Biya €10 D Kuma Kokarin Da Yayi a Tsohuwar Qungiyar Tashi.

Barcelona Na Kokarin Duk Yanda Zaayi Taga Ya Kasance Dan Wasanta

Wannan Ba Kowa Bane illa Frenkie Dejong, Wannan Labari Yazo Ne Daga Majiyar Da Bata Yada Qarya Wato #MUNDO-DEPORTIVO,  Qungiyar Barcelona Tafi Shaawar Daukarshi Akan Kowane Dan Wasa a Wnnan Kakar Domin Kuwa Domin Kuwa Maganarda Akeyi Yanzu Anfitarda Albashi Wanda Zaa Rika Baiwa Dan Wasan Idan Har Ya Amince, Dukda Cewa Manyan Qungiyoyi Suna Nemansa Kamar PSG, Manchester City Da Bayern Munich.

Xavi Hernandez Shine Mutum Wanda Ya Kara Hutawa Barcelona Cewa Su Kawo Shi, Ga Kadan Daga Cikin Kalaman Xavi Akan.
Ina Matukar Kaunarsu Sosai Shida Abokin Wasan Sa Wato Delight Saboda Kwararru Ne Basu Cika Barar Da Dama Ba, Basu Bata Kwallo a Hannunsu Shiyasa Nake Shaawarsu a Qungiyar Barcelona.

A Yanzu Haka Qungiyar PSG Na Cikin Tsaka Mai Wuya.

Qungiyar Tana Cikin Jerin Qungiyoyin Da Talauci Ya Fara Hayemusu a Wannan Qarnin Da Muke Ciki, Hakan Ya Biyo Bayan Sakamakon Sayen Gadarar Da Sukema Dan Wasa a Matsayin Su Masu Kudi, To Yanzu Mganarda Ake Sun Zama Talakawa 😃😃

An Bayyana Cewa Idan Har Qungiyar Tanason Kanta Domin Ci Gaba Da Buga Champions League To Sai Ta Ajewa Asusun Qungiyar Akalla Euro Million 170m.

Wannan Doka Tazo Ne Daga Masu Kula Da Wasan Na Zakarun Nahiyar Turai, a Yanzu Haka Qungiyar Ba Suda Wadannan Kudin Da Zasu Iya Kai Kansu Domin Cika Sharudan Da Ake Bukata Na Ci Gaba Da Buga Gasar.

Hanya Mafi Sauqi Muddin Sunason Suci Gaba Da Buga Champion League To Dolene Sai Sun Dai Daya Daga Ckin Yan Wasansu #NEYMAR Koh #MBAPPE, a Yanzu Haka Mai Qungiyar Watau Naseer Yana Shirin Yadda Wannan Alamari Zai Shawo Kansa Domin Ganin Ya Nemi Kudinda Zai Samu Damar Cika Dokokin, Ta Hakane Suke Shirin Rabuwa Da Wadansu Guda NEYMAR Koh MBAPPE. Wannan Labari Yazo Ne Daga Majiyarda Ke Kasar Faransa Cewa Basu Mallaki Komaiba a Akwatin Qungiyar.

Samuel UMTITI Yana Fama Da Matsananci Ciwo Gwiwa Wato (Knee) Irin Ciwonda Ya Tilasta Tsohon Captain Din Qungiyar Barcelona Wato PUYOL.

Tun a Farkon Wannan Wata Likitocin Qungiyar Suka Bada Tabbacin Cewa Umtiti Zai Dawo Catalonia Daga Qasar Qatar Amman Hakan Baiyiyuba Haka Zalika Suka Kara Bada Sanarwar Cewa Zai Dawo a Jiya 24 December Amma Baiyiyuba, Daga Karshe Sun Tabbatarda Cewa a Ranar 30 December Shekarar Da Muke Ciki Zai Dawo.

Rabon Da Samuel Umtiti Ya Bugawa Qungiyar Wasa Tun a Karawar Qungiyar Da Atletico Madrid a Gasar Laliga Kuma Wannan Wasa Shine Wasa Na 7 Kacal Da Ya Bugawa Qungiyar a Kakar Wasa Ta Bana.

Bisa Matsalar Raunin Da Yake Fama Dashi Hakan Yasa Qungiyar  Ta Amshi Aron Dan Wasan Baya Na Valencia Mai Suna Murillo Dan Kasar Colombia.

Tarihin Da Cristiano Ronaldo Ya Aje Wanda Ake Tunanin a Shekara Mai Kamawa 2019 Lionel Messi Zai Iya Karya Su.

Lionel Messi Da Cristiano Ronaldo Sun Kasance Yan Wasa Biyu Da Ake Alakanta Su Da Yan Wasan Da Baa Taba Irinsu Ba a Tarihin Kwallon Kafa, Dan Kuwa Cikin Shekara Goma (10) Da Suka Gabata Sun Mamaye Dukkan Wani Kyauta Da Ake Samu a Gasar Kwallon Kafa.

TARIHI NA FARKO SHINE

1. Mafi Yawancin Kwallaye Uku (3) a Wasa Daya Hatrick Kenan, Dan Wasan Na Portugal Ya Aje Wannan Tarihi a Gasar Laliga Day Messi Ya Kasa Karya Shi Inda RONALDO Yayi Hatrick Sau 34, Shi Kuwa Messi Yanada 31 Hatrick a Tarihi.
Ana Ganin Wnnan Tarihi Sai Yafi Dukkanin Sauran Tarihin Wuyar Karya Wa, Duba Da Yanzu Haka Dan Wasan Baya Kasar Spaniya Ta Hakane Aka Bayyana MESSI Sai Ya Karya Tarihin Cikin Sauri Ba Sai Anje Ko Inaba a Shekara Mai Kamawa 2019.

2. DAN WASA MAFI YAWAN CIN KWALLAYE A SEASON DAYA.
Wannan Tarihi Yanada Matukar Karyuwa a Wajensa Kamar Yadda Aka Bayyana Duba Da Yadda Haryanzu Bai Kama Kafarsa Ba Kuma Dukkansu Ba Daina Cin Kwallaye Sukayi Ba, Cin Kwallo 20 a Gasa Ba Wasa Bane. Sai Dai Idan Akwai Wanda Zai Iya Karya Tarihin Na RONALDO To Bai Wuce MESSI Din Ba.

3.TARIHI NA UKU SHINE
Mafi Yawancin Kwallaye a Gasa Ta Champions League Wanda Aka Bayyana Su a Rubuce Kamar Shekara 2017 Da RONALDO Yaci Kwallaye 17, Amman Ana Tsammanin Messi Zai Iya Karya Tarihin a Wannan Shekarar Da Zamu Shiga 2019.

ZAA BADA SANARWAR KAMMALA CINIKIN KUNGIYAR FC ANDORRA DA GERRARD PIQUE YAKEYI A RANAR 3 GA JANUARY.

Gerard Pique Na Shirin Zama Mai Kaso Mafi Tsoka a Hannun Jarin Qungiyar FC ANDORRA, Ta Hanyar Kamfaninsa Kosmos, Kuma Ana Kyautata Zaton Wannan Lamari Zai Kammala Ne a Ranar 3 Ga Watan January Shekarar 2019.
Cinikin Zai Yiyu Ne Dazarar Aka Canza Wasu Dokokin Wasannin Na Kungiyar, Wanda Ake Ganin Zaayi Hakan a Ranar Alhamis, Kuma Kafin Nan Mahukuntar Kungiyar Zasu Bayyana Amincewarsu Da Sabon Tsarin a Filin Taron Masu Fadi Aji Na Qungiyar a Ranar 29 Ga Watan December.
Satin Da Ya Gabata Ne Diari De Andorra Ke Bayyana Pique Na Shirin Sayen Wannan Qungiya, Kuma Sai Gashi Yanzu Jaridar RAC1 Ta Riga Da Ta Bayyana Ranar Da Sanarwar Zatazo a Hukumance.

Da Zarar Wannan Lamari Ya Kammala, Dan Wasa Gabri Garcia Da Albert Jorquera Zasu Dawn Takawa Qungiyar Leda Kamar Yadda Ake Tsammani a Yanzu Haka Qungiyar Itace Ta 10, a Rukuni Na 2 a Bisa Teburin Gasar Farko Da Ake Bugawa a Sashin Cataluniya.

YA KUKAJI WANNAN KAFCEN KUMA NA SAN BAKU RASA TA CEWA...

CHAKWAKIYA TSAKANIN LIONEL MESSI DA CRISTIANO RONALDO A SHEKARAR NAN TA 2018.

Lionel Messi Da Cristiano Ronaldo Suna Yar Tsere, Domin Mazge Juna a Kokarin Wanda Yafi Kowa Zura Kwallo a Shekara (TOP SCORER) Na Wannan Shekarar 2018.
Tauraron FC BARCELONA Lionel Messi Yanada Kwallaye 48 a Kalandar Wannan Shekarar, Yafi Tauraron Juventus RONALDO Da Kwallaye 4.

Amman Ba Hanzari Ba Gudu Ba Domin MESSI Bayada Sauran Wasa Ko Daya Wadda Ta Rage Masa a Yayinda Shi Kuma RONALDO Yake Da Sauran Wasanni Biyu Da Suka Rage Masa Ka Fin Mu Shiga Sabuwar Shekara.

Daga Cikin Wadannan Dakarun Kowa Yanada Kyautar Ballon d'or Har Guda 5, Sai Dai a Tseren Kyautar Takalmin Zinari (GOLDEN SHOE), MESSI YANA GABAN RONALDO, Idan Aka Hada Da Wanda MESSI Ya Dauka a Satin Da Ya Gabata MESSI Yanada (5), RONALDO Kuma Yanada (4).

MESSI Yaci Wadannan 50 Goals Ne Ga Qungiyar Ta Qasa Da Waje a Wannan Shekarar Ta 2018. RONALDO Kuma Yaci Kwallaye 47 Din Ne Ga Tsohuwar Qungiyarshi Madrid, Juventus Da Portugal. Yana Da Sauran Wasanni Uku Da Suke Rage Masa a Wannan Shekarar Da Muke Ciki Ta 2018.

Masu Biyowa Wadannan Mazaje Guda Biyu Baya Sune Robert Lewandowski Na Qungiyar Bayern Munich Da Yake Da Kwallaye 42, Sai Dan Wasan Atletico Madrid Da Yake Da Kwallaye 40, Sai Harry Kane Yanada Kwallaye 38, Amman Yanada Ragowar Wasanni Biyu Da Tottenham. Shine Ya Mamayi Messi a Shekarar Bara Da Kwallaye 56, Inda Shi Kuwa Messi Yake Da 54.

An Zabi Kwallon Ivan Rakitic a Matsayin Kwallo Mafi Kyawu a Wasannin Rukuni Wato Group Stage Da Aka Kammala Na Gasar Cin Kofin Zakarun Turai.

Ivan Rakitic Ya Samu Wannan Nasara Ne Da Kyakykyawar Kwallon Da Ya Jefawa Qungiyar Tottenham Kuma Itace Magoya Baya Suka Zaba a Matsayin Kwallo Mafi Kyawu.

Rakitic Ya Samu Wannan Nasara Ne Bayan Ya Doke Abokan Wasanshi Ousmane Dembele, Mauro Icardi, Da Cristiano Ronaldo Na Juventus.

An Zabi Kwallon Ivan Rakitic a Matsayin Kwallo Mafi Kyawu a Wasannin Rukuni Wato Group Stage Da Aka Kammala Na Gasar Cin Kofin Zakarun Turai.

Ivan Rakitic Ya Samu Wannan Nasara Ne Da Kyakykyawar Kwallon Da Ya Jefawa Qungiyar Tottenham Kuma Itace Magoya Baya Suka Zaba a Matsayin Kwallo Mafi Kyawu.

Rakitic Ya Samu Wannan Nasara Ne Bayan Ya Doke Abokan Wasanshi Ousmane Dembele, Mauro Icardi, Da Cristiano Ronaldo Na Juventus.

Ko Was Zaiyi Nasara Tsakanin Dembele Da Rakitic?? 

An Bayyana Kwallayen Ivan Rakitic Da Ousmane Dembele a Cikin Mafi Kyawu Da Zaa Zaba a Wannan Rukuni Da Aka Kammala a Gasar Cin Kofin Zakarun Turai.

Ivan Rakitic Ya Samu Wannan Nasara Ne Bayan Jefa Kwallo Ta Ban Mamaki a Ragar Tottenham, Irin Kwallon Nan Da Ake Kira Da Volley Ball a Filin Wasa Na Wembley a Wasan Da Barcelona Ta Lallasa Tottenham 4-1,  Shi Kuma Dembele Aka Zabi Kwallonsa Da Ya Jefa Ma Tottenham a Camp Nou Yasamu Aka Zabi Kwallonsa Da Zaa Baiwa Kyautar Kwallo Mafi Kyau a Wasannin Rukuni.

Haka Zalika Kwallon Da Mauro Icardi Ya Jefawa Qungiyar Tottenham Itama Ta Shiga Jerin Ckin Kwallaye Mafi Kyau,  Sai Kwallon Da Cristiano Ronaldo Ya Jefawa Qungiyar Manchester United Itama Tana Dai Ckin Kwallon Da Ake Ganin Zaa Iya Zaba.

Yan Wasan Barcelona Ne Suka Fi Yan Wasan Ko Wace Qungiya Cin Kyautar Takalmin Zinare

1. Ronaldo Na Brazil Yaci Kyautar a Shekarar 1996/1997

2. Andre Messi Shine Yaci Kyautar a Karo Na 2 a Barca, a Shekarar 2010/2011.

3. Lionel Messi Shi Kuma Yaci Kyautar a Shekarar 2012- 2013- 2017- 2018

4. Luis Suarez Shine Yaci Kyautar a Shekarar 2015/2016.

Takaitattun Labarun Qungiyar Kwallon Kafa Ta Barcelona

Da Farko Zakuji Cewa Da Yiyuwar Dan Wasan Tsakiyar PSG Mai Suna #Andrien-Rabiot Ya Tsallako Zuwa Qungiyar Barcelona a Kyauta Free Transfer Kenan Yayinda Aka Jiyo Dan Wasan Yana Bayyana Wa Manema Labarai Aniyarsa Ta Canza Sheka, Haka Zalika Dama Dai Tuni Aka Jiyo Coaching Na Barcelona Yana Fadar Cewa Kungiyar Ta Gama Yarjejeniya Da Qungiyar #PSG Akan Batun Canza Shekar Matashin Dan Wasan.

A Wata Majiyar Kuma Zakuji Cewa Badakaren Jarumi Mai Tsaron Gida Na Barcelona Wato #Jordi Alba Ya Gargadi Qungiyar Juventus Da Ta Daina Bata Lokacinta Na Zawarcin Da Take Yimasa, Ya Kuma Fada Cewar Yana Nan Daram Qungiyar Barcelona Bazai Iya Kasancewa a Wata Qungiyar Ba Muddin Ba Barcelona Ba Ce.

Daga Karshe Kuma Zakuji Cewa #Messi Ya Doke Abokin Hamaiyarsa Wato #Ronaldo Wajen Yawan Lashe Kyautar Takalmin Zinare Inda #Messi Yake Da 5, #Ronaldo Kuma Yake Da 4

Neymar Jr

Fitaccen Dan Wasar Kwallon Kafa Ta #PSG Dan Kasar Brazil Kuma Tsohon Dan Wasan #Barcelona Wato #Neymar Jr, Ya Sha Alwashin Da Wowa Tsohuwar Qungiyar Tasa Wato #Barcelona a Watan Junairu Inda Ya Bayyanawa Mahukuntan #PSG Din Karara Sai Dai Haryanzu Mahukuntan Barcelona Basu Gamsu Da Hakan Ba.

Saura Kiris #Barcelona Su Cimma Matsaya Da Ajax Akan Dan Wasanta Mai Suna  #Frenkie Dejong Inda Ake Sa Ran Dan Wasan Kan Iya Tahowa a Watan Junairu.

Dan Wasan Celta Vigo Robert Mazan, Wanda Ya Karbi Rigar Lionel Messi Bayan Tashi Daga Wasa Tsakanin Barcelona Da Celta Vigo. Yayi Posting Din Hoton Rigar Da Ya Karba Hannun Messi, Tare Da Rubuta Nagode Sarki.

Amman Daga Bisani Sai Yanemi Gafarar Hakan Da Yayi, Ganin Irin Raddin Da Magoya Bayan Celta Vigo Ke Yin Mishi.

Sunce Baya Iya Kwallo Bayan Dagawar Wadannan Xavi Da Iniesta

To Amman Sai Gashi Yanzu Ya Kasance Shi Kadai Kan Iya Komai a Harakar Kwallon Kafa. Ko Kunsan Cewa Maganarda Pele Yayi Akan Messi Hakan Ne Yasa Duk Qungiyar Da Ya Hadu Da Ita Baya Yimata Da Sauqi.

Pele Yace Messi Baya Iya Cin Kwallo Idan Ba Da Kafarshi Ta Hagu Ba Kawai Ta Hakanne Yanzu Messi Ya Samu Damar Cin Kwallaye Har Kusan 4 Da Kafar Dama Daga Lokacinda Pele Yayi Maganar Zuwa Yanzu, Saboda Ya Nunawa Pele Cewa Shi Na Daban Ne Kuma Dan Baiwa.

A Yanzu Haka An Tsaida Ranar Ci Gaba Da Buga Wasar Zakarun Nahiyar Turai.

BARCELONA Vs LYON

Zaa Fara Wasan Ne a Ranar February 19 Shekarar Da Zata Kama a Kasar Faransa.

A Wasa Na Biyu Kuma Zai Kasance a Ranar 13march 2019 a Babban Birnin Barcelona Dake Catalunya Camp Nou Kenan.

An Haramtawa #Dembele Kashe Waya Ko Kuma Saka Ta Silent Cikin Dare, Wannan Hukunci Ya Biyo Bayan Matakin Da Qungiyar Ta Dauka Na Kiran Matashin Ta Waya a Duk Sa Fiya Ranar Atisaye.

Dan Gudun Kara Samun Wani Jinkiri Daga Dankalin Sha-kushe, Anan Gaba a Lokacin Atisaye Kamar Yadda Aka Samu a Baya.

Barcelona Zasu Fara Saka Coutinho Da Dembele a Lokaci Daya Lokutan Wasa.

Hakan Ya Biyo Bayan Sakamakon Sauye Sauye Na Karin Kwazo Daga Dukkansu Musamman Ma Ousmane Dembele Wanda Tauraruwarsa Ke Haskawa a Yanzu.

Abun Ne Ya Zama Rikita Squad Wannan Al amari Zai Kasance Na Barkata Zubi Ko Kuma Gyarashi a Yayin Hakan Ne Valverde Yake Kokarin Gyara Arthur Melo Da Arturo Vidal Amma Haryanzu Ya Kasa.

Thomas Vermaleen Ya Koma Injury.
Bayan An Tashi Daga Wasan Da Barcelona Ta Lallasa Qungiyar Lavente Likitoci Suka Tabbatarda Dan Wasan Ya Samu Injury Wanda a Kalla Zai Shafe Wata 1 Yana Jinya.

An Bawa Messi Kyautar Takalmin Zinare.
Golden Boot Kenan Kyauta Ce Wadda Ake Baiwa Dan Wasa Wanda Yafi Kowa Zura Kwallaye a League. 

Wannan Shine Karo Na Biyar a Tarihi Da Yasamu Wannan Kyautar Kuma Babu Wani Dan Kwallo Wanda Yafishi Wannan Yawan Kyautar.

Akwai Yiyuwar #De Zerbi Shine Zai Maye Gurbin Ernesto Valverde a Barcelona.

Rahotanni Da Suka Mamaye Jaridu a Jiya Lahadi Kasar Spaniya Da Kuma Kasar Italy Sun Alakanta Fasihi Mai Horasda Qungiyar Sassaulo #Roberto De Zerbi, a Matsayin Wanda Zai Maye Gurbin Ernesto Valverde a Barcelona.

Roberto De Zerbi Yana Samun Yabo Bisa Yadda Yake Iya Sauya Salon Wasar Qungiyar Cikin Kwarewa Kamar Pep Guardiola, Haka Zalika Mutum Ne Mai Fasaha Ta Ban Mamaki a Fagen Horaswa Domin Izuwa Wannan Lokaci Da Ya Karbi Qungiyar Sassaulo Yana Gab Da Dorasu a Mataki Wanda Zasu Iya Buga Gasar Zakarun Nahiyar Turai Domin  Kuwa Maki 3 Tazararsu Da Qungiyar Da Ke Mataki Na 4.

Wannan Shine Babban Rahoto Da Yaja Hankalin Magoya Bayan Qungiyar Kwallon Kafa Ta Barcelona.

Ronaldo Zai Dawo Real Madrid

Bayan Raba Rukuni Na Qungiyoyi Da Aka Gabatar a Wasar Zakarun Turai Wato Champion League, Inda Aka Hada #Juventus Da #Atletico Madrid Hakan Shi Yaba Ronaldo Damar Zuwa Birnin Madrid Wanda Rabonsa Da Zuwa Birnin Tun Lokacinda Yabar Qungiyar Real Madrid.

Duk Wani Shiri Da Qungiyarmu Zatayi Akan Messi Toh Shirme Ne a Cewar Kociyan #LYON

Inda Yaci Gaba Da Cewa Duk Yin Hakan Bata Lokaci Ne In Har Zaka Tsaya Kayi Tunanin Ta Yanda Zaka Dakatarda Messi Domin Shi Dan Wasa Ne Mai Wayo Da Kwarewa.

Amman Ina Kyautata Zaton 100% Akan Zamu Nasara a Kansu a Duka Wasanni Biyu Da Zamu Buga Dasu a Gasar Kofin Nahiyar Turai. A Cewar BRUNO GENESIO.

An Tambayi Tauraron Dan Wasan Qungiyar Kwallon Kafa Ta Ajax Matthijis Delight.

Wanda Yafison Yayi Wasa Dashi a Team Daya Tsakanin MESSI DA RONALDO,  Sai Yace Yafison Yayi Wasa Zichyet a Qungiyar Su Ta Ajax.

Bana Tunanin Barin Ajax a Wannan Season Din, Bansan a Wane League Zan Sake Yin Wasa Anan Gaba Ba, Amman Kuma Nasan Cewa Zanyi Wasa a Wata Qungiya Nan Gaba.

Wace Qungiya Ce Wannan
Sai Yace Fatan Shi Allah Kasa #BARCELONA Ce.

Labari Daga Jaridar BarceBlaugranes Ta Wallafa Labarin Cewa Kungiyar Kwallon Kafa Ta Barcelona Da Real Madrid Na Tsere Kai Da Kai Domin Sonsu Na Daukan Dan Wasan Gaban Man United #Marcus Rashford.  Dan Wasan Baya Samun Damar Wasanni a Kai a Kai Karkashin Jagoranci Jose Mourinho Inda Kotagrin Shi Zai Kare Da Qungiyar a Karshen Wannan Kaka Mai Kamawa.

Qungiyar Kwallon Kafa Ta Barcelona Na Duba Yiyuwar Daukar Dan Wasan Borussia Dortmund Wato #Jordan Sancho Dan Asalin Kasar England.
Dan Wasan Mai Shekaru 19 Ya Koma Qungiyar Borussia Dortmund Ne Dag Qungiyar Man City a Kakar Da Ta Gabata, Inda Kungiyoyi Irinsu Liverpool, Bayern Munich, Real Madrid Keson Daukar Dan Wasan.

Qungiyar Kwallon Kafa Ta Barcelon Na Duba Yiyuwar Maye Gurbin Dan Wasanta #Luis Suarez Da Dan Wasan Gaban Qungiyar Celta Vigo #Maxi Gomez.
Qungiyar Ta Yaba Da Kokarin Dan Wasan a Wasan Da Suka Kara a Ranar Asabar Inda Tace Dan Wasan Salon Wasan Shi Irin Na Na Luis Suarez Ne, Domin Dan Wasan Yasan Raga Kuma Idanuwansa Suna Kan Raga Kowane Lokaci.

Haryanzu Dai Qungiyar Barcelona Bat Kara Yin Wata Magana Ba Dan Gane Da Qaramin Dan Wasanta Ba Wato #Munir Elhaddadi Akan Makomar Dan Wasan Biyo Bayan Inda Yarjeneniyar Sa Zata Kare Da Qungiyar a Karshen Wannan Kakar.