Yanda Kasuyar Kwallon Kafa Ke Gudana a Halin Yanzu

Yanda Kasuwar Saye Da Sayarwa a Harakar Kwallo Ke Gudana.

Da Farko Zakuji Cewa Real Madrid, Barcelona Harda Ma Bayern Munich Duk Suna Rababin Daukar Matashin Dan Wasan Borussia Dortmund Mai Suna Jadon Sancho.

Kungiyar Kwallon Kafa Ta Liverpool Na Zawarcin Dan Wasa Timo Werner Dan Asalin Kasar Germany, Werner Wanda Qungiyoyi Da Dama Irinsu Liverpool, Bayern Munich Da Manchester United, Ke Sa Ido Wurin Son Daukar Matashin Dan Wasan.

Jaridar (Sky Italy) Ta Bayyana Cewa Chelsea Kan Iya Mika Dan Wasanta Alvaro Morata Domin Daukar Dan Wasan Kasar Argentina Gonzalo Higuan a Watan January.

Juventus Tasa Ido Akan Matashin Dan Wasan Ajax Matthijis Delight Dan Kasar Netherland.

Paris Saint Germany Ta Fara Duba Yiyuwar Dauko Dan Wasan Tsakiyar Everton Mai Suna Idrissa Gueye, Anasa Ran Idrissa Gueye Shine Wanda Zai Maye Gurbin Dan Wasa Adrien Rabiot Wanda Ke Yunkurin Canza Sheka Daga Paris Saint Germany Zuwa Qungiyar Kwallon Kafa Ta Barcelona a Watan January Ko a Karshen Season Dinnan.

Real Madrid Na Shirye Shiryen Ta Mikawa Chelsea Tayin Yasan Ta Guda Isco Alcaron Da Matteo Kovatic, Duk Dan Qungiyar Ta Sallamar Musu Da Eden Hazard Dinda Suka Juma Suna Nema, Kovatic Wanda Yake a Matsayin Aro Wato Loan a Qungiyar Kwallon Kafa Ta Chelsea, Real Madrid Na Son Yin Amfani Dashi Wurin Cinma Burinta Na Son Daukar Dan Wasa Eden Hazard a Watan January Ko a Karshen Season Dinnan.

Qungiyar Kwallon Kafa Ta Chelsea Karkashin Jagorancin Maurici Sarri Ta Shirya Kawo Yan Wasa Guda Hudu a Wannan Watan Na January, Cikin Yan Wasan Sun Hada Da Nabil Fekir Na Lyon, Sai Jamie Vardy, Gonzalo Higuan Da Isco Alcaron, Amman Ana Tunanin Higuan a Matsayin Aro Zasu Dauke Shi.

0 comments:

Post a Comment