WANENE DEMBELE
[ Kashi Na Karshe ]

O. Dembele Ya Taka Rawar Gani Musamman a Wannan Kakar Wasannin Inda Ya Zura Kwallaye 12 Cikin Wasanni 27 Daya Bugawa Kungiyar Ta Barcelona Kuma Ya Bada Taimako Anci 5 Dukka a Wannan Kakar Wasannin Ta 2018/19.

Dembele Ya Samu Nasarar Lashe Kofuna 5 Tun Bayan Zuwan Sa Barcelona Wanda Suka Hada Da:
Laliga x1
Copa del Rey x1
Spanish Super Cup x1
Supercoper de Catalunya x1
Trofeo Joan Gamper x1

Haka Zalika a Watannin Da Suka Wucene Dembele Ya Samu Damar Shiga Sahun 'Yan Wasa 11 Da Kocin Barcelona Erneston Valverde Yake Son Fara Wasa Dasu Inda Ya Bence Abokin Wasan Sa
Philippe Coutinho, Sai Dai Wannan Mataki Da Kocin Ya Dauka Ya Jawo Cece-Kuce a Tsakanin Magoya Bayan Kungiyar Ta Barcelona Wanda Wasu Suna Ganin Hakan Yayi Dai-Dai Wasu Kuma Suna  Ganin Sam-Sam Wannan Ba Dai dai Bane.

Sai Sai Kocin Ya Fito Ya Kare Kansa Da Cewa "Bawai Ina Sa Dembele a Wasane Don Ina Sonsa Ba, Ko Kuma Bana Sa Coutinho Don Bana Sonsa, Sam Wannan Ba Haka Yake ba, Kawai Dai Ina Bawa Kowa Damansa Ne a Kungiyar, Doomin a Baya Can Bana Sa Dembele a Wasa Kuma Hakan Ya Jawo Min Kalubale Daga Wajen Magoya Bayan Sa, Amma Daga Baya Na Gyara.

Sai Dai KASH!! a Ranar 20/1/2019 O. Dembele Ya Hadu Da Wani Iftila'i Na Rauni Da Yaji a Idon Sawunsa Na Hagun a Wasan Da Barcelona Ta Sheke Kulob Din Leganes Daci 3-1 a Gasar Cin Kofin Laliga Zagaye Na 20,
Bayan Binciken Likitocin Da Kuma Gwaje-Gwajensu Sun Tabbatar Da Cewa Dembele Zai Shafe Sati Biyu Yana Jinya, Yayin Da Bazai Sami Daman Buga Wasanni 4 Da Kungiyar Zata Buga Kafin Ya Warke.
[ AL'HAMDULILLAH ]
Wannan Shine Kadan Daga Cikin Tarihin Ousmane Dembele, Gwarzo Dan Kasar France.
Shugaba Muhammadu Buhari Ne Ya Fadi Wadannan Kalaman a Yau: 

Daga Real Sani Twoeffect Yawuri.

"Nayi Tsammanin 'Yan Adawa Zasu Nemo Kwafin Takardar Da Na Bayyana Kadarorin Dana Mallaka Suyi Kokarin Nuna Inda Nayi Rashin Gaskiya.

Nasan Inada Kariyar Dokar Tsarin Mulki, Amma Idan Akwai Inda Na Fadi Karya a Cikin Takardar, To Nayarda Kada Kariyar Dokar Tsarin Mulkin Ta Bani Kariya Ko Hanani Yin Murabus.

Ya Kamata Mudinga Mutunta Dokokin Tsarin Mulkin Kasarmu Domin Bamu Da Wata Kasar Data Fita.

Ko Kuma Bari ince,  Ni Dole Na Mutunta Dokokin Kasar Nan Domin Banida Wata Kasar Data Fita.
WANENE DEMBELE ???
[ Kashi Na Hudu 4 ]
A Ranar 14/3/2018 Dembélé Ya Fara Zura Kwallon Sa Ta Farko a Barcelona a Wasan Cin Kofin Zakarun Turai Zagaye Na Biyu Wanda Barcelona Ta Lallasa Kulob Din Chelsea Daci 3-0, Sannan a Ranar 17/4/2018 Dembele Ya Zura Kwallo a Wasan Da Barcelona Ta Tashi Canjaras Wato 2-2 Da Kulob Din Celta Vigo, Wanda Itace Kwallon Sa Ta Farko Da Yaci a Gasar Laliga Tun Bayan Zuwan Sa Barcelona, Haka zalika Ranar 9/5/2018 Dembélé Ya Sake Zazzaga Kwallaye Har Biyu Rigis a Wasan Da Barcelona Ta Bawa Villarreal Kashi Daci 5-1 a Filin Wasa Na Camp Nou.
Dembélé Yayi Nasarar Lashe Kofuna Biyu
Wanda Suka Hada Da Laliga League, Da Kuma
Copa Del Rey, Duka a Cikin Kakan Wasansa Ta Farko a Barcelona, Inda Yaci Kwallaye Hudu Cikin Wasannin 24 Daya Bugawa Kungiyar. A Ranar 12/8/2018 Dembélé Shine Yaci Kwallo Ta Biyu a Wasan Karshe Na Kofin Spanish Super Cup Da Suka Doka Da Kulob Din Sevilla, Wanda Cin Da Yayine Ya Bawa Kulob Din Ta Barcelona Daman Daukar Kofin Kuma Karo Na x17 Wajen Daukar Kofin Kenan.
Ousmane Dembélé Ya Cimma Nasarori Dadama a Kungiyar Kwallon Kafa Ta Barcelona Musamman a Cikin Kakar Wasanni Ta 2017/18, Kuma Yayi Nasarar Zura Kwallallaki Da Dama Ciki Harda Kwallon Da Ya Zura a Wasan Da Barcelona Ta Doke
PSV Eindhoven Daci 4-0 a Gasar Kofin Zakarun Turai Wanda Aka Buga a Filin Wasa Na Camp Nou.
Ko a Ranar 28/10/2018 Dembele Yayi Nasarar Bada Taimako Ga Arturo Vidal Wajen Cin Kwallon Karshe Wanda Barcelona Tayiwa Babbar Abokiyar Hamayyarta Duka Wato Real Madrid Daci 5-1 a Wasan Kofin Laliga Wanda Ake Masa Kirari Da El Clásico.
WANENE DEMBELE ???
[ Kashi na Uku 3 ]
Ranar 27/5/2017 Borussia Dortmund Ta Buga Wasan Karshe Na Kofin DFB-Pokals Da Kulob Din
Eintracht Frankfurt Inda Sukayi Nasara Daci 2-1 Haka Yabawa Dortmund Samun Nasarar Daukar Kofin Karo Na Hudu Kenan a Tarihin Kungiyar, Dembele Shine Ya Fara Zura Kwallon Ta Farko a Wasan Sannan Ya Nuna Bajinta Matuka Hakan Yasa Aka Ambaceshi a Matsayin [ Man Of The Match] Na Wasan, a Karshe Kakar Wasa Na 2016/17 Dai Kungiyar Borussia Dortmund Ta Bayyana Dembele Amatsayin Gwarzon Dan Wasan Dortmund Na Shekarar 2017.
Sannan Aka Karramashi Da Kyautar [League's Rookie Of The Season Award].
A ranar Litinin 25/8/2017 Barcelona Ta Bada Sanarwar Yarjejeniyar Da Suka Cimma Da Borussia Dortmund Akan Sayen Ousmane Dambele Kan Kudi Fam Miliyan 135.5, Hakan Tasa Ya Zama Dan Wasa Na Hudu Mafi Tsada a Duniya, Barcelona Ta Sayi Dembele Ne Don Ya Maye Mata Gurbin Neymar Jr Wanda Ya Sauya Sheka Zuwa Kulob Din Paris st-Germain Ta Kasar Germany.
A Ranar 9/9/17 Ya Fara Buga Wasa a Barcelona a Wasan Da Suka Doke Kulob Din Espanyol, Daci 5-0 a Filin Wasa Na Camp Nou, Ya Shigo Wasan Ne a Minti Na 68 Da Wasan Inda Yayi Canjin Gerard Deulofeu, Kuma Shine Ya Taimakawa Luis Suarez Wajen Zura Kwallon Ta Biyar a Ranar.
A Ranar Asabar 13/9/17 Dembélé Ya Samu Rauni a Kafarsa a Wasan Da Suka Gwabza Da Getafe, Raunin Na Dembélé Yayi Tsanani Hakan Yasa Ya Tafi Jinya Har Na Wata Hudu, a Ranar 2/1/2018 Likitocin Barcelona Suka Bada Tabbacin Warke War Dembélé, Sai Dai Sati Biyu Da Dawowarsa Daga Jinyar Yasake Samun Wani Raunin Inda Ya Tafi Jinyar Sati Hudu.
WANENE DEMBELE ???
[ Kashi Na Biyu 2 ]
A Ranar 9/1/2016 Dembélé Ya Kara Ska Kwallo a Wasan Da Sukayi Nasara Daci 2-0 Da Kulob Din Les Rouges Et Noirs, Haka Zalika Ranar 6/3/2016 Dembélé Ya Sake Cin Kwallo Uku Rigis Wato Hat-trick a Wasan Da Suka Doke Kulob Diin Nantes a Filin Wasa Na -Derbe Breton, Kuma Shine Kwallo Uku Daya Fara Ci a Wasa Daya.
Saboda Kokarin Da Dembélé Yakeyi Da Kuma Salon Da Yake Nunawa a Wasa Yasa Sporting Director Na Kungiyar Ta Rennes Wato Mikaël Sivestre Yake Danganta Shi Da Sanannen Dan Wasan Nan Na Kulob Din Juventus Wato Cristiano Ronaldo, Inda Yake Cewa "Salon Wasan Dembélé Dai-Dai Yake Dana Ronaldo Lokacin Yana Manchester United"
A Ranar 12/5/2016 Dembélé Ya Canja Sheka Daga Rennes Zuwa Kulob Din Borussia Dortmund Dake Germany Wanda Suke Buga Kofin Bundesliga, Sai Dai Bai Tare a Kungiyar Ba Sai Ranar 1/7/2016, A Ranar 14/8/2016 Dembélé Ya Fara Bugawa Dortmund Kwallo a Wasan Da Suka Doke Kulob Din Bayern Munich Daci 2-0 a Kofin DFL–Supercup, Dembélé Ya Fara Cin Kwallon Sa Ta Farko Da Dortmund Ranar 20/9/2016 a Wasan Da Suka Doke Kulob Din VFL Wolfsburg Daci 5-1 a Filin Wasa Na Volkswagen Arena.
Sannan a Ranar 22/11/2016 Dembélé Yaci Kwallon Sa Ta Farko a Gasar Champions League a Wasan Da Sukayi Raga-Raga Da Kulob Din Legia Warsaw daci 8-4 Tun a Zagayen Rukuni Na Gasar.
A ranar 26/4/2017 Dortmund Ta Buga Wasa Da Kulob Din Bayern Munich a Wasan Daf Da Na Karshe Na Kofin DFB-Pokals, Dembélé Ya Taka Rawar Gani a Wasan Inda Yaci Kwallo Daya
a Minti Na 74 Da Wasa, Sannan Yabada Taimako Ga Aubameyang Yaci Kwallon Duk Dai a Wasa Daya Inda Hakan Ya Bawa Kungiyar Ta Borussia Dortmund Zuwa Wasan Karshe Na Gasar Kofin DFB-Pokals.
WANENE DEMBELE ?
[ Kashi Na Daya 1 ]
Cikakken Sunansa Mansour Ousmane Dembélé, An Haifeshi a Shekara Ta 1997 a Garin Vernon, Dake Kasar France, Yanzu Yana Da Shekara 22 Da Haihuwa, Yana Da Mahaifiya Mai Suna
Fatimata Dembélé, Sannan Yana Da Babban Aboki Mai Suna Paulinho Tsohon Dan Wasan Barcelona.
Dembelé Mabiyin Addinin Islama Ne, Sannan Bashi Da Dabi'ar Shan Sigari Ko Kuma Giya, Haka Zalika Bashi Da Matar Aure, Hattama Budurwa Dembélé Bashi Da Ita, Dambélé Yana Da Mota Mallakin Kansa Kirar Range Rover, Mutum Ne Mai Sha'awar Son Wasan Kwallon Kafa Tun Yana Yaro, inda ya bayyana Ronaldinho Da Messi Amatsayin Manyan 'Yan Wasan Da Yafi Qauna a Duniyar Tamola.
Dembélé Ya Fara Buga Wasan Kwallon Kafa Ne a Qungiyar Madeleine Éureux a Shekara Ta 2004 Zuwa Ta 2009, a Shekara Ta 2010 Ya Canja Sheka Zuwa Kulob Din Rennes, Sai Dai Dembélé Yana Buga Wasane a Karamar Qungiyar Ta Rennes Wanda Suke Buga Kofin Championnat De France Amateur, Dembélé Ya Taka Rawar Gani a Kulob Din Rennes Inda a Ranar 6/9/2014 Ya Taimakawa Kungiyar Tasa Wajen Doke Kulob Din Breton Reveals Daci 2-0, Duk Da Cewa Ya Shigo Wasanne a Minti Na 76 Inda Yayi Canjin Zana Allée.
Yaciwa Rennes Kwallaye 13 Cikin Wasanni 18 Daya Buga a Shekararsa Ta Farko Biyo Bayan Kwallaye Uku Dayaci Ranar 16/5/2015 a Wasan Da Suka Doke Kulob Din Herouville Daci 6-1.
A ranar 6/9/2015 Dembélé Ya Fara Bugawa Babban Qungiyar Rennes Wasa a Kofin Ligue 1, a Wasan Da Sukayi Da Kulob Din Angers, Inda Yayi Canjin Kamin Grosick, a Minti Na 85.
A ranar 22/11/2015 Ya Fara Zura Kwallon Sa Ta Farko a Kofin Ligue 1 a Wasan Da Suka Tashi Canjaras 2-2 Da Kulob Din Bordeaux, a Filin Wasa Na Roazhon Park.
WANENE COUTINHO?
[ Kashi na karshe ]
A Ranar 6/1/18 Liverpool Ta Bada Sanarwar Cimma Yarjejeniyar Da Sukayi Da Barcelona Kan Sayen Dan Wasan Kan Kudi Euro £142m, Hakan Ne Yasa Ya Zamo Dan Wasa Na Uku Da Suka Fi Tsada a Duniya.
Bayan Zuwan Countinho Barcelona Alokacin Gwajin Lafiyarsa Angano Cewa Yana Dauke Da Rauni a Cinyarsa Hakan Tasa Countinho Yin Jinya Harna Tsawon Sati Uku 3.
Bayan Samun Lafiyarsa Ya Fara Buga Wasa a Barcelona Ranar 25/1/18 a Kofin Copa Del Rey a Wasan Da Barcelona Ta Doke Tsohuwar Kungiyar Sa Ta Espanyol Daci 2-0, Ya Shigo Wasanne a Minti Na 68 Inda Yayi Chanjin Captain Din Kungiyar Wato Andres Iniesta, Da Taimakon Suarez Countinho Ya Samu Daman Zura Kwallonsa Ta Farko a Barcelona Ranar 8/2/18 a Wasan Da Suka Buga Da Kulob Din Valencia Zagaye Na Biyu a Kofin Copa Del Rey.
Ranar 28/10/18 Ya Sake Zurawa Barcelona Kwallo a Wasan Da Suka Sheke Babbar Abokiyar Hamayyansu Wato Real Madrid Daci 5-1, a Gasar Laliga Wanda Ake Mata Take Da El Clásico, Countinho Ya Bugawa Barcelona Wasanni 52 Tun Bayan Zuwansa Kungiyar Inda Ya Zura Kwallaye 16.
Haka Zalika Ya Samu Nasarar Lashe Kofuna Guda 3 Wadanda Suka Hada Da Laliga Cup 1, Copa Del Rey 1, Da Kuma Spanish Super Cup 1, Sai Dai a Baya-Bayan Nan Kocin Barcelona Ernesto Valverde Ya Fuskanci Cecekuce Da Suka Dagawa Magoya Bayan Countinho Akan Cewa Baya Son Amfani Da Dan Wasan Yafi Son Amfani Da Abokin Wasansa Wato O. Dembélé, Yayin Da Wasu Suke Ta Yada Labarai Da Cewa Coutinho Zai Tashi Daga Kungiyar Saboda Wannan Dalilin, Sai Dai Kocin Ya Fito Ya Musanta  Hakan Da Cewa Ko Kadan Wannan Ba Gaskiya Bane Na Cewar Yafi Son Dembélé Kawai Dai Ana Dai Bawa Dembélé Tasa Daman Ne Don Shima Aga Tasa Basirar.
[ALHAMDULILLA]
Kadan Kenan Daga Cikin Tarihin Philippe Coutinho.
Na Dau Damarar Yin Wannan Rubutu Ga Dangina Don Wayarda kansu Akan Wani take Da Ake kira....
#NEXT_LEVEL!!!
#Hakika Siyasa Rigar Yanci ce kuma tanan ne kadai Al'uma keda Damar Zabar Duk Dan'takarar Da Suke So Ya Jagorancesu Ga Dukkan Wasu Matakai Na Gwamnati Tundaga kansila Har Zuwa Shugaban kasa,
Yakai Dan'uwa kasani Kuri'arka Makamin Yakar Zalunci ce kuma Itace Next Level Ba Dan takaraba ko Hosta ko Jam'iya, kasani Next Level Bazai Iya kawoma Chanji Ga Ainifin Nagartaccen Shugaba Adili ba, kuri'arka Itace Next Level Saboda Itace Zata Can zama Daga Mutumin Banza zuwa Na kwarai,
Next Level Kirkirace kuma Sirrin Dake kunshe Cikin Wadannan kalmomi Manufar Itace Ayi #Sak Idan bamu mantaba2015 Ana (#Jiki_Maganyi) Malammai Da Sauran Masu fada Aji Sunyi Fama Wurin Fadakarda Al'uma Cewa kar Muyi Sak Mu tsaya Muyi Tunani Akan Cancanta, Mu Zabi Nagari Masu kishin Talakawa Masu kishin Addini
Hakan Zaisa Musamu Shawagabanni Nagari Masu Tausayin mu. Muka Zo Mukayi Sak Daga Baya Muka Dawo Cizon Dan'Yatsa, #PDP ko #APC Babu Shegiyar uwa, kuma babu Partyn Musulunci ko kafirci, Acikin Ya'yan Jam'iya Ake Samun Shugaba Adili kuma Acikin tane Ake Samun Barayi,
Maudu'i na Shine Mu fahimci Ginshikin Wanann Bayani... Ba Muce Asoke Taken Next❌Level ba, Manufa Anan Itace Bazamuyi Sak ba Saboda Akwai Waanda Basu Cancanci su Sake Mulkin mu ba, Kowa Yayi Mana Daidai Zai Gani.
Next Level===Kayi Siyasar Akida.
Next Level===Kuri'arka Yan'cinka.
Next Level===Ka Zabi Mai Gaskiya.
Next Level===kayi Wake-Da-Shinkafa.
Next Level===kayi Siyasar Hangen Nesa. Wannan Shine Next Level Allah ka bamu Ikon Ganewa
WANENE COUTINHO?
[ Kashi na Uku 3 ]
Countinho Ya Samu Nasarori a Kulob Din Liverpool Wanda a Nanne Aka Fara Kiransa Da [Magician] Wato Matsafi Amma a Kwallon Kafa, a Shekara Ta 2015 Ne Ya Lashe Kyautar Gwarzon Dan Wasan Shekara Na Kungiyar Ta Liverpool, Wanda Har Sai Da Tsohon Dan Wasan Duniya Pelé Ya Jinjina Masa Da Cewa Matashin Dan Wasa Ne Mai Tasowa.
Countinho Ya Fara Buga
Wasan Sa Na Farko a Liverpool Ranar 11-Feb- 2013, Wasan Da Liverpool Din Ta Doke West Bromwich Albion Daci 2-1 a Filin Wasa Na Anfield, Wanda Yayi Chanjin Stewart Downing a Minti Na 77 Da Wasan, Haka Zalika Countinho Ya Fara Zura Kwallon Sa Ta Farko a Liverpool Ranar 17/2/213 a Wasan Daya Buga Minti 90 Inda Suka Doke Kulob Din Sweansea City Daci 5-0, Sannan a Ranar 2/3/213 Countinho Ya Sake Zurawa Liverpool Kwallaye Biyu a Wasan Da Suka Doke Wigan Athletic Daci 4-0.
Countinho Bai Tsaya Anan Ba a Watan 3 Yaba Da Taimako Wato {Assist} Akaci Kwallo Biyu Wasan Da Liverpool Din Ta Doke Aston Villa Daci 2-1, Kokarin Da Yayine Yasa Kulob Din Liverpool Ta Ambaceshi Amatsayin Gwarzon Dan Wasa Na Watan March Wato [Liverpool's Player Of The Month For March], a Turance.
Countinho Yayi Abubuwan Birgewa a Rayuwarsa Da Liverpool a Shekara Ta 2014— 2015—2016— Wanda Saboda Rashin Lokaci Bazan Iya Kawo Muku Suba.
A shekara Ta 2017 A Watan 8 Barcelona Tayi Kokarin Saye Coutinho Kan Kudi Euro £72m.
Amma Kulob Din Liverpool Yaki Amincewa Da Wannan Tayin.
Hausawa Na Cewa "Mai So Baya Zuciya" Hakan Tasa Kulob Din Barcelona Sake Kai Tayin Dan Wasan Karo Na Biyu Duk a Shekara Ta 2017 Din Karkashin Jagorancin Director Na Kungiyar Wato Albert Soler Kan Kudi Euro £183m, Amma Duk Da Haka Liverpool Din Taki Sallamar Da Dan Wasan.
WANENE COUTINHO?
[ Kashi na Biyu 2]
A Shekara Ta 2008 Ne Kulob Din Inter Milan Ta Kasar Italiya Ta Saye Dan Wasan Kan Kudi Euro Miliyan €4. Wanda Daga Baya Kuma Suka Bada Aron Dan Wasan Ga Tsohuwar Kungiyarsa Ta Vasco Da Gama.
Ashekara Ta 2010 a Watan July Dan Wasan Ya Dawo Kulob Din Inter Milan Lokacin Yana Da Shekara 18 Da haihuwa, Countinho Yadawo Inter Milan Karkashin Mai Horas Da 'Yan Wasa Rafael Benítez, Da Kuma Chiaman Din Kungiyar Wato
Massimo Moratti, Inda Suke Masa Lakabida Cewa [Ginshikin Inter Mai Zuwa].
Countinho Ya Fara Zura Kwallonsa Tafarko Ne a Inter Milan a Bugun Tazara Wato [Free-Kick] Ranar 8 Ga Watan Mayu Shekara Ta 2011, Wasan Da Sukayi Nasara Akan Fiorantina, Daci 3-1, Countinho Ya Kara Zura Kwallonsa Ta Biyu a Inter Milan Ne Ranar 19 Ga Watan November 2011 Wanda Sukayi Nasara Akan Kulob Din Cagliari Daci 2-0.
A Shekara Ta 2012 Inter Milan Din Ta Sake Bada Shi Aro Zuwa Kulob Din Espanyol Ta Kasar Sipaniya.
Countinho Ya Shafe Kakar Wasa Guda a Kungiyar Ta Espanyol, Inda Ya Fara Buga Wasan Sa Na Farko Ranar 4 February 2012, Inda Suka Tashi Canjaras Wato 3-3 Da Kulob Din Athletic Bilbao Karkashin Mai Horas Wa Mauricio Pochettino, Countinho Yaci Kwallaye 5 Cikin Wasanni 16 Daya Buga Kungiyar Kafin Ya Dawo Gida Inter Milan a Karshen Kakar Wasanni Ta 2012.
A shekara Ta 2013 Watan January Ya Koma Liverpool Da Taka Leda Akan Kudi Euro Miliyan £8.5. Ko Dayake Kafin Zuwan Dan Wasan Liverpool Kulob Din Southampton Sun Nuna Sha'awar Daukar Dan Wasan Amma Yaki Amincewa Yace Fa Lallai Sai Liverpool, Bayan Tabbatar Da Cinikin Sa Akan Yarjejeniya Mai tsayi Kungiyar Ta Dauki Riga Ta Bashi Mai Dauke Da No 10.
WANENE COUTINHO?
[ Kashi Na Daya 1]
Cikakken Sunansa Philippe Countinho Corriea, An Haifeshi a Garin Rio De Janeiro Dake Kasar Brazil Ranar 12 June 1992 Wanda Yanzu Yake Da Shekara 27, Countinho Yana Da Mahaifi Mai Suna
Ze Carlos Countinho, Sai Kuma Mahaifiya Mai Suna Dona Esmeralda Countinho, Inda Yake Da Dan Uwa Mai Suna Christian Countinho Leandro Countinho.
Haka zalika Countinho Yana Da Matar Aure Guda Daya Mai Suna Aine Countinho, Wanda Ya Aure Ta Ashekara Ta 2012 Inda Yake Da Yara Biyu Masu Suna Kamar Haka:
Philippe Countinho,
Maria Countinho,
Philippe Countinho Mabiyin Dddinin Christer Ne Bashi Da Dabi'ar Shan {Cigarette} Sigari, Sai Dai Yakan Sha Giya Wani Lokaci, Haka Zalika Countinho Yana Da Babban Aboki Sadio Mane Wanda Yake Taka Leda a Kulob Din Liverpool Dake Kasar England.
Countinho Mutum Ne Mai Sha'awar Son Kwallon Kafa Tun Yana Yaro Inda Yake Yawan Fadin
Ronaldinho Da Maradona Amatsayin 'Yan Wasan Daya Fi Kauna a Duniyar Tamola, Sannan Countinho Yana Da Sha'awar Kallon Bidiyo Na Wasanni Dama Na Sauran Shirye-Shiye, Haka Zalika Countinho Mutum Ne Mai Son Sauraron Wakar Matashin Mawakin Nan Dan Kasar America Wato Justin Bieber.
Idan Muka Koma Ban Garen Bugun Tamola Kuma Philippe Countinho Ya Buga Wasa a Kungiyoyi Da Dama Yayin Da Ya Cimma Nasarori Dadama Inda Har Ake Masa Lakabi D [Little Magician The Kid] Wato Karamin Matsafi Amma Fa a Kwallon Kafa Saboda Alokacin Ya Tashi Da Jarabar Iya Kwallon Kafa Sosai. Countinho Ya Fara Buga Wasa Ne a Shekara Ta 1999 Zuwa Shekara Ta 2008 A Kulob Din Vasco D Gama, Wanda Aka Kirkireta Ranar 12-Aug-1898 Wanda Yanzu Take Da Shekara 121 Da Kafuwa.

"Abin da matasa ke buƙata shi ne yanayi mai kyau domin su gina kansu ta yadda za su bada gudummawa wajen cigaban Najeriya - Sarkin Gombe

Daga Haji Shehu

Mai martaba Sarkin Gombe Dr Abubakar Shehu Abubakar lll wanda ya kasance babban bako wajen Taron "Daily Trust Dialogue" karo na 16 wanda akayiwa lakabi da "Youth and Democracy" a turance, taron ya samu halartar ministoti, manyan yan jaridu, masu sharhi akan al'amuran yau da kullum, manyan yan siyasa da kuma wakilan kungiyoyi daban-daban na ciki da wajen Najeriya.

Yayin taron, an gabatar da jawabai da suka shafi rayuwar matasa da siyasa da kuma matsaloli da matasa ke fuskanta a rayuwar yau da kullum.

Da yake jawabi, mai martaba Sarkin Gombe ya bayyana muhimmancin tallafawa al'umma musamman matasa tare da zayyano irin nasarorin da ya cimma ta fuskar inganta rayuwar al'ummarsa kama daga matasa musamman yaran marasa galihu cikin al'umma, inda yake cewa "Abin da matasa ke buƙatar shi ne yanayi mai kyau domin su gina kansu ta yadda zasu bada gudummawa wajen cigaban Najeriya. Amma muddin aka rasa wannan, to, mu kasance cikin shiri domin sakamakon da bazai zo da dadi ba"

Sarkin ya cigaba da cewar "Na cimma nasarori a bangaren ilimin yara mata da rage adadin yara marayu da marasa galihu wadanda basa makaranta ta hanyar gina makarantun Islamiyya da sanya yara 3,000 a makaranta domin ilimin zamani.

Basaraken ya zayyano nasarorin da ya cimmawa ta fannoni daban-daban ciki har da fannin kiwon lafiya, inda ya gina asibiti da kuma sanya kayan aiki domin kulawa da lafiyar al'umma.

Kungiyar kwallan kafa ta Burusian Dortmund ta kammala daukar Dan wasa Depende Leonardo daga Kungiyar kwallan kafa ta Bocca junior dake kasar Argentina.
████████████████████████
Dan wasan tsakiyar Kungiyar kwallan kafa ta spur mousa Dembele nakan hanyarsa ta zuwa kasar China domin kammala tafiyarsa zuwa Kungiyar kwallan kafa ta Beijing Goun dake buga gasar super league inda akesa ran Dan wasan zaikai kimanin euro milian 11.
███████████████████████
Coach din Arsenal zai iya barin dan wasa Ozil domin ya bar kungiyar, dan wasan dai yafi kowa karbar albashi a Arsenal din.
███████████████████████
Chelsea zasu bukaci a basu kudi kamar Pounds Million 100 akan dan wasansu Hazard idan dan wasan ya nuna sha’awarsa na barin kungiyar.
Amma Wani Rahotanni Sun Bayana real Madrid Ta Amince Xata Kudin Dan wasan*
███████████████████████
Sakamakon ciwaon da Harry Kane ya samu Tottenham zata iya karbar aron dan wasan Barcelona mai suna Malcom.
███████████████████████
.
Dan wassan gaba na West Ham wato Marko Arnautovic ka iya komawa kungiyar kwallon kafa ta Shanghai SIPG dake China.
███████████████████████
Savilla sunce asun hakura da daukan dan wasan Chelsea wato Morata saboda cewar wai dan wasan yayi musu tsada – sun bada Euro Million 40 an dawo musu da ita.
███████████████████████
Sakamakon haka Morata zai rage kudin da ake biyansa ya koma Atletico Madrid – amma Atletico Madrid din kuma dole sai sun sayar da wani daga cikin yan wasansu.
███████████████████████
Golan Manchester United yace zai cigaba da zama a kungiyar amma yana bukatar Man United din su kara masa albaashinsa zuwa 300,000 Pound a sati.
███████████████████████
Yawa-yawan yan wasan Manchester United suna son Solskjaer yaci gaba da zama coach din kungiyar da din-din-din.
███████████████████████
Chelsea sun kammala yarjejeniya da dan wasan Zenith dan Argentina mai suna Leandro dan shekara 24.
███████████████████████
Liverpool, Tottenham, da Everton suna neman dan wasan gefe na kungiyar kwallon kafa ta Club Brugge dake Belguim mai suna Danjuma.
███████████████████████
PSG suna neman dan wasan tsakiya mai buga lamba 4, kuma sunce suna son dankan dan wasan Everton dan asalin kasar Senegal mai suna Idrissa.
███████████████████████
Dan wasan tsakiya na Ajax mai suna De Jong yana daf da komawa PSG akan kudi Pounds Millions 67.
██████████████████████████████

Kalaman Shugaban Hukumar Kwallon Kafa Ta Gasar Laliga Akan Lionel Messi

JAVIER TEBAS
A Gaskiyar Magana Idan Har Ana Maganar Dan Kwallon Duniya To Meessi Nee Kuma Ina da Tabbacin Messi Zai Kasance a Allon Tarihi Na Tarihin Kwallon Duniya .

Zanso Ace Zai Kammala Buga Kwallonsa a Gasar Ta Laliga Domin Kuwa Ddinmune Dan Wasan Duniya Da Babu Kamarsa Ya Kasance Daga Gasarmu Ya Fito.

Ina Fatan Messi Kasancewarka a Barçelona Domin Kuwa Shine Abun Burgewa Kafara Buga Kwallo a Kulob Kagama a Nan

Bacelona Ba Zata Sayi Dan Wasan Girona Ba Watau STAUNI Da ake Alakanta ta Dashiba Inji.

MUNDO DEPOTIVO
A Yan Kwana Kinnan Duniya Ta bazu Cewa Barçelona Tana Shaawar Daukar Danwasan Gaban Kungiyar Kwallon Kafa Ta Girona fç Akan Kudi Euro Million 15m Domin Ya Maye Mata Gurbin Danwasanta Daya Koma Kungiyar Sevilla Watau Munnir Elhaddadi

Wannan Lbrn Yazo Yanxu Cewa Barça Bazata Sayeshiba duba da Wasu Matsololin Sa Guda Biyu Da Suka Fahimta Dangane Dashi

Matsalar Dan Wasan Na Farko Shine
1 * A Gaskiyar Lamari Barçelona Batason Danwasan Domin Kuwa Ga t
Tsufa Ya Fara Jansa Dukda Cewa Tsaran Luiz Suarez Ne Shima Wannan Wani Dalilin Ne Da Yasa Sukace Sun fasa

2. Kudin Da Akamasa Sunyi Yawa Dubada Yadda Suka Sallamar Da Danwasansu Munnir Elhaddadi Agarabasa Dan Kuwa Cinikin Kamar k
Kyautane Akaba Sevilla ...
Domin Kuwa Haryanzu Sun fi Ganin Cinikin Danwasan Gaban Chelsea Watau Morata Duk Da Cewa Anfi Alakantashi Amatsayin Aro Zaizo.

JADAWALIN RANAKUN FITA YAKI NEMAN ZABEN SHUGABA BUHARI

Laraba 16-01-2019 Jihar KWARA da Jihar KOGI.

Alhamis 17-01-2019 Jihar DELTA da Jihar EDO.

Juma'a 18-01-2019 Jihar KADUNA.

Assabar 19-01-2019 Jihar NIGER da FILATO.

Litinin 21-01-2019 Jihar BORNO da YOBE.

Talata 22-01-2019 Jihar SOKOTO da KEBBI

Alhamis 24-01-2019 Jihar ENUGU da ANAMBRA.

Assabar 26-01-2018 Jihar OYO da Jihar OSUN.

Lahadi 27-01-2019 Jihar KANO.

Talata 29-01-2019 Jihar IMO da Jihar ABIA.

Laraba 30-01-2019 Jihar CROSS RIVER da EBONYI.

Alhamis 31-01-2019 Jihar OGUN.

Assabar 02-02-2019 Jihar JIGAWA da GOMBE.

Lahadi 03-02-2019 Jihar KATSINA da ZAMFARA.

Talata 04-02-2019 Jihar EKITI da jihar ONDO.

Alhamis 06-02-2019 Jihar RIVERS  da BAYELSA.

Assabar 08-02-2019 Jihar ADAMAWA da TARABA.

Litinin 11-02-2019 Jihar LAGOS.

Laraba 13-02-2019 NASSARAWA da BINUWAI.

Alhamis 14-02-2019 Rufewa Birnin Tarayya Abuja.

ANKAMA MAYAN 'YAN KASUWAR DAKE DAUKAR NAUYIN 'YAN BINDIGAR ZAMFARA A JAHAR

- 'Yan sanda sun kama wasu mahauta 'yan asalin jihar Zamfara mazauna Legas bisa zarginsu da daukan nauyin 'yan bindigar Zamfara
- Mahautan guda hudu da aka kama sune Alhaji Ago Atine, Alawani Abubakar, Mohammad Sahagari da Bashir Aliyu
- Alhaji Altine ya ce wani Alhaji Naira ne ke sayar masa da shanun da araha shi kuma ya sayar da su da tsada a Legas
- Sashin tattara bayanan sirri na 'yan sanda ya gano cewar 'yan bindigan na amfani da kudin da suke samu daga sayar da shanun satar ne wurin sayo makamai

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta kama wasu mahauta hudu da ke sayar da nama a Agege na jihar Legas bisa zarginsa da daukan nauyin 'yan bindiga da ke kai hare-hare a wasu garuruwa a jihar Zamfara.

The Punch ta ruwaito cewa garuruwan da aka kai harin sun hada da kananan hukumomin Tsafe, Zurmi, Shinkafi Maradun, Mari da Birnin Magaji.
'Yan sandan sunyi ikirarin wadanda ake zargin su ke samarwa 'yan bindigan kudaden da sukae sayan makamai ta hanyar sayan shanun sata daga hannunsu. Wadanda ake zargin sune Alhaji Ago Atine, Alawani Abubakar, Mohammad Sahagari da Bashir Aliyu.

An gano cewar 'yan bindigan da suka kashe mutane da dama sunyi amfani da kudin da suka samu bayan sayar da shanun ne wajen sayo bindigu da wasu muggan makamai daga kasar Libya.
Majiyar Legit.ng ta gano cewa sashin tattara bayyanan sirri na 'yan sandan Najeriya sun damke kwamandan 'yan bindigan ne a Zurmi kuma ya tona yadda 'yan bindigan ke samun kudin sayan makamai.

An kama wadanda ake zargin su hudu ne yayin da suke kokarin sayar da wasu daga cikin shanun satar ga wani mutum.
Daya daga cikin wanda ake zargin, Alhaji Altine ya shaidawa City Round cewa ya saya shanu fiye da 400 daga wani Alhaji Naira. Sai dai ya ce bai san cewa shanun sata bane.

Ya ce, "Alhaji Naira ya aiko min da shanu fiye da 400 ni kuma na sayar masa a mayanka. Na tura kudin zuwa asusun ajiyar bankin Alhaji Naira. Na saya shanun da araha, ya sayar min da kowanne guda a kan N60,000 zuwa N70,000 ni kuma na sayar da kowanne a kan N170,000 zuwa N180,000. Ban san abinda Alhaji ya ke yi da kudin ba kuma ban san shanun na sata bane.

     

# BREAKING_NEWS_LIVE
# PELLIPE_COUTINHO
SuperSport.Com
Fitaccan Dan wasan Barcelona Dan kasar Brazil mai suna Pellipe_Coutinho ya Musanta dangantashi da ake ake da kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta PSG inda yake shaidawa manema labarai cewa bai shirya barin kungiyar ba duk abokin wasansa na Brazil din kuma na PSG wato
# Neymar_Jr yana duk wata bita da kulle wajan janyo hankalin Dan wasan amma duk da haka ya bai da burin barin kungiyar ta # Barcelona a wannan lokacin

<b>MANCHESTER UNITED TAFARA TATTAUNAWA DA WAKILIN DAN WASAN BARCELONA WATO COUTINHO
Kungiyar kwallon kafa ta Manchester united dake kasar England tafara tattaunawa da wakilin dan wasan gaban kungiyar Barcelona wato Phillip Coutinho domin komawar dan wasan manchester united din a wannan kakar.

Dan wasan mai shekara 26 yakoma kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ne daga liverpool akan kudi €160 akakar wasanni data gabata.
Danwasan yarasa gurbin shi a kungiyar ta Barcelona tun bayan zuwan sa akarkashin jagoran cin kociyan Enersto Valverde.

# Munir ya aike dasakon ban kwana mai Sosa Zuciya ga magoya bayan kungiyar kwallon kafa ta Barcelona.
.
Duk da bai bayyana komaiba a yayin da kungiyar kwallon kafa ta Sevilla ta gabatardashi amma hakan bai hana Munir Elhadadi yin amfani da shafinsa na Twitter don yin ban kwana ga magoya bayan kungiyar kwallon kafa ta Barcelona.
.
Cikin sakon da Munir ya akai yafadi cewa <b>Nazo nan tin ina yaro Dan shekara 16 da buri tareda kyakykyawan fata kamar kowane matashi daya samu damar shiga makarantar koyar da wasanni ta Lamasia, sau biyu ina barin kungiyar ina kuma dawowa domin na kara jarraba sa'ata."
"Ayanzuma nasake tafiya saide a wannan lokaci na kudircewa kaina natafi kungiyar dazanyi
# kwallo ."
.
A karshe Munir yarufe dacewa <b>Akoda yaushe Kuna nan a # Raina ."
.
Munir yakoma Sevilla akan kudin dabai taka kara ya karyaba domin kuwa an sallamashi akan Euro miliyan €1m da yan doriya.
.


████████████████████████
*
*
Tsohon dan Wasan Real Madrid Pepe ya koma kungiyar kwallon kafa ta FC Porto pre transfer
████████████████████████
Barcelona sun kammala daukan dan wasan baya na Toulouse dake France mai suna Todibo*
████████████████████████
Real Madrid ta kammala sayen matashin dan wasan Manchester City mai suna Brahim Diaz a Wannan Mako
████████████████████████
Chelsea na da sha'awar daukar dan wasan gaban na Real Madrid Karim Benzema, a cewar jaridar Mirror
████████████████████████
Rahotanni daga italiya na cewa kungiyar kwallon kafa ta Arsenal na yunkurin daukar dan wasan Juventus Mehdi Benatia.
████████████████████████
Tsohon Coach din Arsenal wato Winger zai koma coach din kasar Qatar.
████████████████████████
Bayern Munich tana daf da daukan dan wasan Chelsea wato Callum Hudson.
████████████████████████
Chelsea suna neman dan wasan AC Milan wanda yake a matsayin aro a Savilla wato Andre Silva.
████████████████████████
Barcelona sun tabbatar da cewa zasu sayar da Malcom da Danis Suarez.
████████████████████████
Arsenal zasu mayar da tsohon dan wasansu mai suna d Edu director na kungiyar.
███████████████████████
Rahotanni Sun Bayana Qungiyar Qwallon Qafa Ta Manchester United Tana son Daukar Dan Wasan Barcelona Coutinho Yabayya rashin jindadin Sa a Qungiyar*
████████████████████████
Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta tura wakilanta zuwa kasar Portugal domin suga yadda dan wasa Eder Militao yake buga wasa a baya a kokarin da kungiyar takeyi na ganin ta siyi dan wasan
████████████████████████
Kungiyoyin Atletico Madrid da Balencia dake kasar Sipaniya suna zawarcin dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Aledis Sanches, kamar yadda rahotanni suka bayyana daga kasar ta Sipaniya
████████████████████████
Tsohon kocin Manchester United Jose Mourinho ya yi watsi da tayin da kungiyar kwallon kafa ta Benfica
████████████████████████
Cecs Fabregas Zai Koma Qungiyar Qwallon kafa Ta Dake Faransa Monaco*
████████████████████████
Cecs Fabregas Zai Koma Qungiyar Qwallon kafa Ta Dake Faransa Monaco*
████████████████████████
Dan Wasan Qungiyar Qwallon kafa ta Liverpool Moreno Na Son Barin*
████████████████████████
Chelsea tana dab da daukan dan wasan gaba na AC Milan wato Higuain.
████████████████████████
Shuganan Chelsea Abramovic yace Icardi shine wanda yafiso Chelsea su dauka a January.
████████████████████████
Inter Milan zata sayar da Perisic don samun kudin sayen dan wasan Real Madrid wato Modric.
████████████████████████
Tottenham sunce duk wanda zai sayi dan wasa Erikson sai ya bada kudin daya kai Pounds Million 225.
████████████████████████
Dan wasan gaba na Tottenham mai suna Llorenti zai iya komawa Atletico Bilbao.
████████████████████████
Atletico Bilbao dai suna son dawo da dan wasan Manchester United mai suna Heirera zuwa kungiyar, sai dai dan wasan yafison ya cigaba da zama a Old Trafford din.
████████████████████████
An gayawa Manchester United su jira zuwa karshen kakar wasa ta bana domin daukan dan wasan baya na Napoli wato Koulibaly.
████████████████████████
Manchester City zasu karawa Komapany kwantaragi.
████████████████████████
Bayern Munich sun tabbatar da daukan dan wasan France dake buga wasansa a VfB Stuttgart mai suna Benjamin Pavard.
████████████████████████

Daga Malam Aminu Ibrahim Daurawa Assalamu Alaikum. Ga wasu dan Tunatarwa ,Wanda Naga Ya Dace Inyi Sharing Da Sauran Mata Don Kowa Ya Amfana.

Dalilai 40 Dake Kawo Saki a Aure

1- Rashin ilimin zamantakewar aure.

2- Al'adu

3- Bidi'o'i (kamar lefe,gara d.s)

4- Rashin binciken halin miji kafin aure

5- Rashin binciken halin mace kafin aure

6- Matsalar iyayen miji

7- Matsalar iyayen mace

8- Matsalar dangin miji

9- Matsalar dangin mace

10- Rashin tsafta

11- Rashin iya kwalliya

12- Rashin iya magana

13- Rashin iya ciyarwa

14- Rashin iya kwanciyar aure

15- Rashin adalci

16- Goyon kaka ('yar shagwaba)

17- Auren kisan wuta

18- Zaman gidan haya

19- Ruwan ido wajen neman aure

20- Cin amanar aure

21- Auren bariki

22- Auren mace dan kudinta

23-Auren dole

24- Talauci

25- Qawaye

26- Zafin kishi

27- Rashin haihuwa

28- Rashin ladabi

29- Shaye-shayen kayan maye

30- Qannen miji

31- Abokan miji

32- Sata

33- Gulma

34- Tsananin damuwa

35- Waya(phone)

36- Rashin lafiyan miji wajen gamsar da mace

37- Rashin lafiyan mace wajen gamsar da miji

38- Sharrin boka

39- Rashin shawara tsakanin miji da mata

40- Aikin mace (kasancewar ta 'yar kasuwa, ma'aikaciyar gwamnati da Sauransu

Kalaman Tsohon Dan Wasan Barçelona Masu Ratsa Zuciya Ga Duk Wani Dan Wasan Barçelana Da Fans

# INIESTA ****Babban Abinda Kungiyarmu Yakamata Mu Kara Nema Ayanxu Shine Champions League Duk Da Cewa Munyi Kokarin Mu Kara Smun Shi Amma Hakan Baiyiyuba .

Amma Inada Tabbas Da Gaske Cewa Wadannan Yan Wasan Da Kungiyar Take Dasu Zasu Iya Cin Wannan Kofin
Authur Melo Kai Gaskiya Wannan Dadakaren Jarumine Matuka Don Kuwa Ko Shakka Babu Kungiyar Anan Gaba Sai Ya Zama Gagara Badau Dan Kuwa Zaa je Dashi Duk Inda Akaso Aje

Gaskiya Naji Dadin Kasancewa Bama Real Madrid Point 10 Tsakani Wannan Ma Wani Alamane Na Tun Yanzu Nasara Ta Fara Tabbata Maana Kofin Na Shirin Zama Na Kungiyar Dukda Cewa Akwai Sauran Kalubalai Anan Gaba
Yin Amfani Da Kananan Yara Masu Tasowa Ababbar Kungiyar Shine Abun Dubawa,  Yanxu Kuma Yakamata Arika Amfani Dasu Domin Karin Sanin Abinda Zai Yuwu Domin Tantance Wanda Akaga Zasu Iya Musamman Ruiq Puiq , Aleña, D Sauransu.

Nayi Kewar Buga Wasa Akungiyar Ta Barçelona Da Birnin Sosai Dukda Cewa Ina Ziyartarsu Akai Akai ......
Dandai Babu Yadda Na Iya Hakan Ina Ganin Shine Daidai Awajena

Messi Bazai Iya Shugaban Ci Ba
inji Maradona

Maradona Wanda Yayi Yayin Tamolarsa Ashekarun Baya Haryanxu Baidauki Messi Amatsayin Wanda Zai Iya Jagorantar Shugaban Ci Ba ..Kawai Zai Dauke Shine Amatsayin Wanda Zai Taimakeku Ga Cinma Nasara Acikin Wasa.

Wannan Kalamai Da Maradona Ke Sukar Messi Din Ya Samo Asali Ne Tun Awasannin Gida Watau Kasarsu T Argentina Domin Kuwa Messi Bai Cika Korafe Korafe Ba Amatsayinsa Na Mai Jagorantar Yan Wasa

Maradona Ya Amsa Wasu Tambayoyi Ne Ga Yan Jarida Ciki Harda Kalamai Dayayi Akan Messi Din,
Ga Kadan Daga Cikin Abinda Yake Fada
<b>MARADONA
MESSI Haryanxu Yana Amataki Na Babban Dan Kwallon Duniya Amma Idan Har Akazo Wajen Shugaban Ci To Baisan Komai Ba.

HAHAHAA TO SAIME DAN BAI IYA JAGORANTAR SHUGABAN CI BA
AI KUMA YA IYA JAGORANTAR MUTANE GA NASARA
GAKA TSOHO AMMA TSOHON BANZA SAI KISHIN TSIYA.

Real Madrid Ta Dauki Brahim Diaz Daga Manchester City

Real Madrid Ta Kammala Daukar Brahim Diaz Daga Qungiyar Manchester City Kan Yarjejeniyar Sama Da Shekara Shida.
A Ranar Litinin Madrid Ta Sanar Da Daukar Dan Wasan Mai Shekara 19, Bayan Da Likitocinta Suka Tabbatar Da Lafiyarsa.

Diaz Mai Buga Tamaula Daga Tsakiya Ya Fara Wasa a Malaga Daga Nan Ya Koma Manchester City Da Murrza Leda Yana Da Shekara 16 a 2015.
Dan Wasan Tawagar Spaniya Ya Buga Wa Matasa 'Yan 17 Da 19, Inda Yanzu Yake Tare D 'Yan Shekara 21

Real Ta Gabatar Da Shi Gaban Magoya Bayanta, Inda Diaz Ya yi Godiya Da Tarbar Da Akayii Masa, Sannan Ya Buga Kwallaye Cikin 'Yan Kallo.
A Karshen Kakar Bana Ne Yarjejeniyar Diaz Za Ta Kare a Ettihad Wdda Ya Buga Wa Wasa 15,
Sai Dai Baui Yadda Ya Tsawaita Kwantiragin Da City Ta Babatar Masa Ba.

Neymar Jr  Zai Dawo Tsohuwar Qungiyar Shi Barcelona.

A Rahotannin Damuke Samu Yanzun Nan Daga Kasar Spaniya Na Nuni Da Cewa Tsohon Dan Wasan Barcelona Wanda Yake Taka Leda a Kulob Din P.S.G Wato Neymar Jr, Zai Iya Dawowa Tsohuwar Kungiyar Tasa Da Taka Leda, a Kakar Wasa Mai Zuwa.

Gidan Radio Na Catalunya Radio, Itama Ta Bayyana Wannan Rahoton Da Cewa Matashin Dan Wasan Mai Shekaru 26 Yayi Magana Da Mai Kula Da Walwalalan 'Yan Wasa Na P.S.G Wato
Andre Cury, a Watan Da Ya Gabata Kafin Bikin Kirsimeti Kan Yiyuwar Komawar Tasa Filin Wasa Na Camp Nou Da Murza Leda.
'
Rahoton Dai Ya Kara Da Cewa Neymar Ya Nuna Nadamarsa Ta Barin Kulob Din Na Barcelona, Sai Dai Yanzu Yace Ba Abinda  Yake So Sama Da Yakoma Tsohuwar Qungiyar Tasa.

Neymar Shine Dan Wasa Mafi Tsada a Duniya Wanda Kulob Din P.S.G Ta Saye Shi a Hannun Qungiyar Kwallon Kafa Ta Barcelona Kan Zunzurutun Kudi Har Euro Million £198. A shekara Ta 2017.

[Karanta Yanzu] Yadda Zakayi Idan WAEC Original Result Dinka Ya Bata

Jama'a Assalamu alaikum a yau zamuyi magana akan yadda mutum zaiyi idan WAEC Original Result dinsa ya bata, sai a biyomu.

Idan ka duba jikin WAEC Original result zaka ga an rubuta cewa idan har ya bata to WAEC ba zata kara baka wani irin wannan result dinba.

Haka kuwa abin yake indai ka batar dashi to WAEC din zata shafawa idonta  toka tayi halin ba sani ba sabo domin kuwa ba zata baka wani irin wannan sakamakon ba.

Duk sanda wani abu ya taso maka da wani organisations ko hukumomi ke bukatar wannan result din to sai dai su rubuta takardar nema ga Hukumar WAEC, bayan wani lokaci hukumar WAEC zata aikawa da wannan organisation ko hukuma cewa Wane-wane tabbas yayi wannan jarrabawar da kuma karin bayani a rubuce, duk sanda mutum yake bukata sai yayi wannan tsarin.

A shekarar 2015 Hukumar WAEC ta canja sabon tsari cewa idan takardar ka ta bata.
Sabon tsarin 2015 shine mutum zai tafi hukumar WAEC ka sana musu cewa WAEC dinka fa ta bata.
Zaka tafi da hoton passport guda biyu.
Zaka cike form sannan ka biya N20, 000, WAEC zata buga maka sabon result irin wanda ya bata, ana kiran wannan result din da "Attestation" zaka ga an rubuta a jikinsa da jan biro, banbancin su kenan da na asalin.

Wannan itace hanyar da Shugaban kasa Muhammadu Buhari yabi aka dawo masa da sakamakon jarabarwar sa da ya bata, sai dai shi Baba Buhari har Office aka kai masa, kai kuma babu wanda zai kawo maka har gida.
Zaka jira har WAEC ta gama sannan ta aiko da ita jiharka sai kaje ka karba shikenan.

Shawarata ga wanda jarrabawarsa ta bata:
1. Mutum yaje yayi police report.
2. Sannan yayi court affidavit.

Allah ya kiyaye batan jarabarwarmu Amin.

Basheer Sharfadi
Social Media Strategist
12-12-2018.

[Fasahar Zamani] Yadda Zaka Nemi Scholarships Ta Wayar Salula

Kamar yadda muka sha fada duniya a yanzu anyi cigaba fiye da yadda muke tsammani domin ko yaushe kara zuwa ake da sabbin fasahohi iri-iri.

Wato Bahaushe yayi gaskiya da yace “Indaranka Ka Sha Kallo”

Yadda Tsarin Yake:
Tsarine da zai baiwa dalibi dama ya shigar da bayanansa cewa shine wane dan aji kaza a makaranta kaza a bangare kaza, shikenan cikin ‘yan dakiku zai kawo maka jerin scholarships a wannan yanki namu na Africa abinda ya rage maka kawai sai nema.

Tsarin yana lura da yanki da kuma matakin karatun mutum kamar wanda ya gama Sakandire ko mai digiri da mai masters d.s sannan ya baiwa mutum dai-dai dashi a irin salon nan da malam Dan Hausa ke cewa “Dai-dai ruwa dai-dai tsaki”.

Yaya Ake Yin Tsarin?:
Ka shiga Play Store a wayarka sai kayi searching application mai suna “SomaApp” shikenan kayi installing dinsa a wayarka, kana shigar da bayanan ka, shi kuma Malam SomaApp zai lalubo maka jerin scholarships da suka dace da kai.

Game da SomaApp:
Wani kamfani mai suna SomaApp Technologies Company Limited dake kasar Tanzania ne suka kirkire shi.

Wani abin mamaki shine yadda turawa suka dinga korafin cewa don me su ba’a saka nasu yankin ba?
Wato dai wannan abune da ‘yan Africa sukayi wanda suka kere turawa kuma a fasahar zamani.

Izuwa yanzu akwai mutane sama da dubu goma 10,000 dake amfani da wannan application din a duniya.

SomaApp dai zai taimakawa dalibai da kuma iyaye wajen cin gajiyar tallafin karatu wanda hankalinsu ma bai kai gareshi ba, don haka iyaye da dalibai sai a dage.

Allah ya bada sa’a.

Basheer Sharfadi
Social Media Strategist.
13-12-2018.

[Cigaba] Yadda Zakayi Amfani Da Application (kamar WhatsApp & Instagram d.s) Sama Da Guda Daya A Wayarka

'Yan uwa Assalamu alaikum yau za muyi magana akan yadda mutum zaiyi amfani da Applications na wayarsa sama da guda daya a waya guda daya.

Wato dai irin salon nan da 'yan gayu keyi a yanzu Baby ta gansu Online a wancan sim din sannan suyi magana da wani Sim din.

In kun fahimta tsarin zai baiwa mutum damar bude account a facebook sama da guda daya kuma ya lura dasu ba tare da yayi log out ba, Haka su Twitter, WhatsApp, Insta d.s.

Dukkan apps dake wayarka zaka iya sakasu sama da sau daya a wayar.

Yadda Ake Yi Shine:
Kaje Play store ka nemi application na "Morchat".
Sai kayi installing shikenan kamar yadda kuke gani a hoton dake kasa.

Idan Allah ya kaimu Gobe zamuyi magana akan Yadda Mutum Zai Nemi Scholarships ta Wayarsa.

Basheer Sharfadi
Social Media Strategist.
12-12-2018.
https://play.google.com/store/apps/details?id=info.cloneapp.mochat.arm64

Shagala: {Za’a Fara Ganin Video Ba Tare Da Ka Danna Ba A YouTube}

A yayin da ake wani yanayin na gudun kece raini tsakanin manyan shafukan sada zumunta na Internet shima shafin YouTube dake zaman shafi na biyu a duniya wajen yawan masu amfani dashi tuni yayi nisa wajen zuwa nasa sabbin sauye-sauyen domin dai gamsar da masu amfani dashi.

Daga cikin sauye-sauyen da zai iya fara aiki kowane lokaci daga yanzu shine tsarin “Auto Play” tsarine wanda kana shiga YouTube sai kaga wani Video to ba sai ka shiga kan videon ba zaka ga yaya videon yake, a’a kawai tsayawa za kayi akan videon shi kuma zai fara haska maka “preview” kai tsaye ba tare da ka danna ba.

Zaka dinga ganin yadda videon yake idan yayi maka sai ka shiga idan kuma baiyi maka ba sai ka wuce, kamar dai yadda kuke gani a Instagram da kuma wadanda ke amfani da tsarin na “Auto Play” a dandalin facebook da kuma Instagram.

A makon da ya gabata ne kamfanin YouTube ya kaddamar da tsarin story mai tsawon mako guda a dandalin.

Allh ya taimaka.
Basheer Sharfadi
Social Media Strategist.

[Cigaba] Yadda Zaka Saka Katin Waya A Wayarka Ba Tare Da Ka Danna Lambobin Katin Ba

Ina wadanda saka katin waya ke ci musu tuwo a kwarya?
Yau ga dama ta samu! Yau Ina tafe da yadda zaka saka kati a wayarka ko duba balance ba tare da ka danna *555 * ko wasu lambobin ba.

Abubuwan da zaka iya yi da wannan tsari:
1. Idan ka siyo katin waya maimakon ka shigar da lambobin to a yanzu Abinda zakayi shine ka haska lambobin a wayarka nan take zai fito maka da lambobin sai ka danna "call" ka zabi layin da zaka sakawa Shikenan.
2. Idan zaka duba balance shima sai ka danna "check airtime" sai ka zabi layin da kake son dubawa shikenan zai budo maka balance.

Yadda Ake Yin Wannan Tsari Shine:
1. Ka shiga play store ka dauko application mai suna "Airtime Loadup - Airtime Loader Scanner"
2. Shikenan sai ka shiga ka fara amfani da abinka.

Allah ya bada sa'a.

Basheer Sharfadi
Social Media Strategist.
10-12-2018.

[Cigaba] Yadda Zaka Magance Matsalar Shan Data Da Cinye Storage Daga WhatsApp Group

Masu amfani da dandalin sada zumunta na WhatsApp sunsha yin korafi akan yadda WhatsApp Group ke cinye musu Data da kuma Space akan waya ta yadda da zarar an turo sakon hotuna ko video to kawai sai ka ga sun hawo kan wayarka kana so ko baka so.

A baya dai mutum yana iya tsayar da sauke hoto/video kai tsaye (auto download) ta yadda sai ka danna sannan zai sauka kan wayarka.

To a yanzu dai whatsApp yazo da sabon sauyi wanda ya fara aiki a iya Group kadai.

Yadda Tsarin Yake:
Shine a yanzu da zarar an turo hoto ko video a group to zaka iya kallar abinka ba tare da ya zo kan wayarka ba ballantana ya cinye maka space sannan yana rage shan Data sosai.

Yadda Ake Shiga Tsarin Shine:
Idan ka shiga whatsApp dinka sai kaje kan Group din da kake son sakawa a wannan tsarin sai ka danne dan yatsanka.
Zai baka zabi sai ka zabi na uku 3 wato "Group Info".
Idan ya bude sai ka shiga "Media Visibility" sai ka zabi "No".
Shikenan ka sanya wannan group din a wannan tsarin.

Allah ya bada sa'a.

Basheer Sharfadi
Social Media Strategist.

TABBAS MUHAMMAD ATIKU ABUBAKAR YA ZIYARCENI.....
Bayani na farko.....
Ga duk mai bibiyar al'amuran da suka shafi wannan shafi nawa yasan cewa a wasu lokutan nakan bayyana cewa akwai matsalolin daya kamata a gyara a cikin siyasar da muke gabatarwa ta kare muraden jam'iyyar APC da Gwamnatin Shugaba Buhari, mukance koda aikin da muke don Allah ne da kuma kaunar gyara kasarmu hakan bazai hana a samar da wata kafar da zaa karawa matasan dake aikin kwarin gwiwa ba, wanda yin hakan zai kara musu fikira da nutsuwar tunkarar abokan adawa a kowanne lokaci, nassan kun san da haka.....
Bayanan da Biyora ya fitar game da sunayen mutanen da zasu taya shugaba Buhari kamfen a zabukan wannan shekara wadanda nake nuna damuwa akan kin saka sunayen mutanen da muke wannan aiki masu yawa daga nan Arewa, ya sanya hakan ya bada dama ga yan jam'iyyar Adawa ta PDP akan su gwada ko zasu samu mutanen da zasu amince suyi tafiyar siyasa dasu tunda dai baa saka su a inda suke ba...
Alhaji Muhammad Atiku Abubakar ya taso tun daga kasar France har zuwa nan Nigeria kai tsaye zuwa birnin Kano inda ya nemi a kirawoni mu tattauna, wannan karramawa ce a siyasance, tabbas mun tattauna har ya sanya in gayyato yan'uwana da abokaina don ya hadamun liyafar girmamawa domin yace bai kamata muyi tattaunawa dashi ba tare daya kyautatawa makusanta na ba....
Ya nemi da in tawo cikin kamfen din temakawa mahaifinsa musammam a wannan yanki namu na Arewa da kasa baki daya.....
GASKIYAR MAGANA.....
Zuwa yau din nan ban gama yanke kowacce shawara ba musammam dayake ina da iyaye, ina da yan'uwa sannan ina da matasa masu yawa da muke gudanar da wannan aiki tare dasu, wanda hakan yasa dole sai na tattauna da kowanne bangare kafin in yanke hukunci a wannan rana ko gobe.....cikin biyu dole ayi daya kodai na amsa wannan gayyata idan na samu goyon baya daga wadanda nake shawara dasu, ko kuma in zauna a inda nake, in sha Allah yau zuwa gobe zan yanke.....
Ina godiya sosai ga dukkan mutanen da suka nuna damuwa akan shaanin daya shafeni a siyasance, su kansu mutanen da suka kasa hakuri suka zageni ko aibatawa ina godiya garesu domin hakan da sukayi ya nuna cewa sun damu dani ne shiisa suka shiga damuwa akaina.....
MASHA ALLAH

Ta Tabbata Cewa Munir Elhaddadi Zai Bar Qungiyar Kwallon Kafa Ta Barcelona

Dan Wasan Gaba Na Barcelona Munir Ya Kulla Yarjejeniya Da Qungiyar Kwallon Kafa Ta Sevilla Domin Komawa Qungiyar a Karshen Wannnan Kakar

Dan Wasa Mai Shekaru 23 Dan Asalin Kasar Spain Yarjejeniyar Shi Zata Kare a Qungiyar a Karshen Kakar Wasanni Ta Bana Inda Qungiyar Ta Barcelona Tayimai Tayin Ya Kara Kulla Yarjejeniya Da Ita Amman Yayi Watsi Da Tayin Domin Samun Buga Wasanni Akai Akai.

Zai Bar Qungiyar Barcelona Ne Sakamakon Karin Kudinda Akayi Masa Da Basu Gamsar Dashi Ba Kuma Hadi Da Karin Rashin Isashen Lokaci a Cikin Fili

Ousmane Dembele Kan Iya Lashe Kyautar Qwarzon Matashin  Dan Wasan Da Yafi Kowa a Laliga

Izuwa Wannan Lokaci Matashin Dan Wasan Qungiyar Kwallon Kafa Ta Barcelona Ousmane Dembele Shine Ya Mamaye Kokarin Dukkan Wani Matashi a Gasar Laliga Domin Kuwa Ma'aunin Kokarinsa Da Kazar Kazar Dinsa Ya Kai Kaso 7.52 Fiye Dana Ko Wane Matashin Dan Wasan a Gasar Laliga

Ousmane Dembele Shine Yafi Mamaye Jaridun Kasar Spaniya Saboda Irin Laifukanda Yake Tafkawa Amman Kuma Kullum Kokarinsa Abun Kara Linkuwa Yakeyi a Qungiyar a Koda Yaushe Cikin Fili

Ousmane Dembele Matashin Dan Wasan Kasar France Ya Buga Wasanni a Bana a Wasar Laliga Kuma Guda 5 Daga Ciki Duk a Sauyi Ya Shigo, Amman Dukda Haka Dan Wasan Ya Assasa Kwallaye 10 a Raga Domin Kuwa Ya Jefa Guda 7 Ya Taimaka An Jefa Guda 3 Wato Assist Kenan

Kwallayen Da Ousmane Dembele Ya Jefa Sunyi Matukar Taimakawa Qungiyar Domin Kuwa Daga Cikin Kwallayen Sa Guda 7 Sun Baiwa Qungiyar Maki Guda 7 Masu Muhimmanci Wanda Idan Ka Ciresu To Qungiyar Kwallon Kafa Ta  Barcelona Zata Koma Mataki Na 3 a Tsewar Jadawali Na Teburin Laliga

Da Yiyuwar Qungiyar Barcelona Ta Dauki Benjamin Pavard a Karshen Kakar Wasanni

Shuwagabannin Qungiyar Kwallon Kafa Ta Barcelona Sun Fara Tattaunawa Da Wakilin Mai Tsaron Bayan Qungiyar Kwallon Kafa Ta Stuttgart's Wato Benjamin Pavard, Domin Daukar Dan Wasan a Karshen Kakar Wasanni Ta Bana.

Dan Wasa Mai Shekaru 22 Dan Asalin Kasar France Mai Buga Gefen Dama, Ya Nuna Kwarewa Da Hazaka a Gasar Cin Kofin Duniya Da Aka Buga a Kasar Russia Inda Har Takai Ga Sunkundu Me Kofin a Shekarar Da Ta Gabata.

Qungiyoyi Da Dama Ne Keson Daukar Dan Wasan, Irinsu Napoli, Real Madrid, Bayern Munich, Barcelona Da Dai Sauransu.

GUANGZHOU EVERGRANDE Ta Mika Tayin €50 Akan Dan Wasa Malcon.

Qungiyar Kwallon Kafa Ta Guangzhou Evergrande Dake Buga Chinese Super League Ta Kasar China Ta Mika Tayin €50 Akan Dan Wasan Gaba Na Barcelona Wato Malcon.

Dan Wasan Dai Yayi Nasarar Dona Wasanni 9 Appearance Tun Bayan Komawar Shi Qungiyar Ta Barcelona, Qungiyar Ta Siyo Dan Wasan Ne a Kakar Da Ta Gabata Daga Qungiyar Kwallon Kafa Ta Bordeaux Akan Kudi €41.

Daga Jaridar Marca

Zakuji Cewa Jaridar Marca Ta Tabbatarda Cewa Shahararren Dan Kwallonnan Wato Lionel Messi Ya Yanke Shawarar Komawa Argentina Da Taka Leda, Dan Wasan Zai Kasance Ckin Squad Din Kasar Argentina a Yayin Da Zaa Fara Doka Gasar Kofin Copa America a Cikin Shakarar 2019 Bayan Ankammala Wasannin Club.

Copa America Kofi Ne Wanda Messi Ya Fuskaci Qalubale Mai Tsanani a Cikinsa Messi Ya Samu Damar Zuwa Final Har Sau Uku 3, Amman Bai Taba Samun Nasarar Daukar Kofin Ba,  Amman Dukda Haka Messi Baiyi Zuciya Ko Fiidda Rai Ga Lashe Kofin Gasar Ba.

Inter Milan Ta Fara Zawarcin Lionel Messi, Abun Dariya Yaro Ya Tsinsti Hakori

Shugaban Inter Milan Ne Yake Ganin Abu Mai Sauki Ne Zuwan Messi a Qungiyar Inter Milan Ta Yadda Abokin Wasan Sa Kuma Abokin Hamayyarsa Wato Ronaldo Ya Baro Kasar Spain Zuwa Juventus.

Ta Hakanne Yake Ganin Cewa Messi Din Zai Iya Canza Sheka Domin Komawa Can Italy Din Ayi Gumurzu Dashi.

Idan Baku Manta Ba Ronaldo Ya Taba Yin Sharhi Akan Messi Cewa Baya Iya Kwallo Ko Wane League Fa Ce Spain, Kalaman Ronaldo Din Na Nuna Cewa Messi Matsoraci Ne a Kwallon Kafa, Amman Lionel Messi Ya Mayar Masa Da Martani Wanda Mai Hankali Ne Kawai Kan Iya Fahimta.