Neymar Zai Dawo Barcelona

Neymar Jr  Zai Dawo Tsohuwar Qungiyar Shi Barcelona.

A Rahotannin Damuke Samu Yanzun Nan Daga Kasar Spaniya Na Nuni Da Cewa Tsohon Dan Wasan Barcelona Wanda Yake Taka Leda a Kulob Din P.S.G Wato Neymar Jr, Zai Iya Dawowa Tsohuwar Kungiyar Tasa Da Taka Leda, a Kakar Wasa Mai Zuwa.

Gidan Radio Na Catalunya Radio, Itama Ta Bayyana Wannan Rahoton Da Cewa Matashin Dan Wasan Mai Shekaru 26 Yayi Magana Da Mai Kula Da Walwalalan 'Yan Wasa Na P.S.G Wato
Andre Cury, a Watan Da Ya Gabata Kafin Bikin Kirsimeti Kan Yiyuwar Komawar Tasa Filin Wasa Na Camp Nou Da Murza Leda.
'
Rahoton Dai Ya Kara Da Cewa Neymar Ya Nuna Nadamarsa Ta Barin Kulob Din Na Barcelona, Sai Dai Yanzu Yace Ba Abinda  Yake So Sama Da Yakoma Tsohuwar Qungiyar Tasa.

Neymar Shine Dan Wasa Mafi Tsada a Duniya Wanda Kulob Din P.S.G Ta Saye Shi a Hannun Qungiyar Kwallon Kafa Ta Barcelona Kan Zunzurutun Kudi Har Euro Million £198. A shekara Ta 2017.

0 comments:

Post a Comment