Barcelona Da Real Madrid Zasu Hadu Sau Biyu a Cikin Kwana Hudu

Zaa Buga Wasanni Biyu Tsakanin Real Madrid Da Barcelona a Cikin Kwana Hudu
An Fitarda Jadawalin Wasan Kusa Da Karshen Gasar Kofin Copa Del Rey ,Inda Kungiyar Kwallon Kafa Ta Barcelona Zata Fafata Da Real Madrid Yayin Da Real Betis Zasu Kece Raini a Tsakaninsu.

Babu Yiyuwar Zaa Buga El Classico a Wasan Karshen Gasar Kofin Kamar Yadda Jama'a Suke Ta Hasashe Sai Dai Zasu Fafata Wajen Neman Wanda Zai Buga Wasan Karshen a Tsakaninsu.

Zaa Buga Wasan Farko a Gidan Barcelona Ranar 6 Ga Satan Fabairu a Filin Wasa Na Camp Nou Da Misalin 9:00pm, Daga Bisani Kuma Zaa Buga El Classico Guda Biyu a Cikin Kwana Hudu a Gidan Real Madrid a Filin Estadio Santiago Bernabeu, Zaa Buga Wasa Na Biyu Na Kofin Copa Del Rey Ranar 27 Ga Watan Fabairu, Sa'annan Kwana Hudu Tsakani a Koma Domin Buga Wasan Laliga.

Rabon Madrid Da Barcelona Su Hadu a Wannan Kofin Tun Shekarar 2014 Inda Real Madrid Tayi Nasara Daci 2-1. Wannan Shine Karo Na Takwas Da Kungiyoyin Biyu Suka Hadu a Wasan Karshe a Wannan Kofin.

0 comments:

Post a Comment